Shugaban Kasa Muhammadu Buhari umarci sabbin Manyan Hafsoshin Tsaro da su kasance masu kishin kasa.
A ranar Laraba ne Buhari ya ba da umarnin yayin ganawarsa ta farko da su a yayin da Ministan Tsaro Bashi Salihi Magashi ya jagorance su zuwa Fadar Shugaban Kasa.
- Kotu ta kwace kudaden tsohon Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari
- An girke sojoji mata 200 a hanyar Abuja-Kaduna
- Na yi wa mata 50 fyade da fashi a gidaje 100
- ‘Duk wanda aka yi wa lambar NIN kafin 2012 sai ya sake’
Ya bayyana musu cewa “Muna cikin yanayi mai hadari saboda haka ku kasance masu kishi, ku yi wa kasa aiki tare da cikakkiyar mubaya’a ga kasa,” a cewar Fadar Shugaban Kasa.
Bayan ganawar, Buhari ya sanar cewa, “Na gana da Manyan Hafsoshin Tsaro a yau kuma suna da cikakkiyar masaniya game da yanayin tsaron da Najeriya ke ciki.
“Na tunatar da su bukatar su zama masu kishin kasa sannan su fifita kula da walwalar sojoji da hafsohi.
“A matsayina na Babban Hafshin Tsaro, ina ba su tabbacin samun cikakkiyar goyon baya.”
Da yake jawabi, Hafsan Hafsoshi, Manjo-Janar Leo Irabor, ya ce za su tsaya kai da fata wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya.
Manjo-Janar Irabor, wanda ya ce za su bauta wa Najeriya kan jiki, kan karfi, ya kara da cewa kare kasar da jama’arta shi ne babban abin da za su sa a gaba.