✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadimar Gwamnan Sakkwato ta rasu sakamakon turmutsutsu a taron PDP

Ta rasu sakamakon turmutsutsu da ya rutsa da ita a wajen taron PDP a Sakkwato.

Hadimar Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, kan ilimin mata, Hajiya Aishat Maina, ta rasu.

Ta rasu ne jim kadan bayan halartar taron yakin neman zaben dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da ya gudana a ranar Talata a Jihar.

Tana daya daga cikin mutanen da turmutsutsu ya rutsa da su a kofar fita daga filin wasa na Giginyu da aka gudanar da taron.

“Wani mai babur ne ya fadi a bakin kofar fita daga filin wasan, hakan ya haifar da turmutsutsu. Tana daga cikin wadanda abun ya rutsa da su,” cewar wata majiya daga Ma’aikatar Yada Labarai ta Jihar.

Da yake karin haske kan faruwar lamarin, Shugaban Hadiman Gwamnatin Jihar, Ibrahim Magaji Gusau, ya ce an ceto marigayiyar sannan aka garzaya da ita Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman Danfodiyo.

Amma abin takaici ta rasu mintuna kadan da kai ta asibitin,” in ji shi.

Magaji ya bayyana marigayiyar a matsayin jaruma kuma mai hazaka da rikon amana.

“A lokacin taron muna tare amma ban san cewar wannan shi ne lokaci na karshe da zamu sake haduwa ba,” a cewarsa.

Ya yi addu’ar Allah Ya yi mata rahama.

Kafin rasuwarta, Hajiya Aishat ta rike mukamin Shugabar Kungiyar Mata ’Yan Jarida ta Kasa (NAWOJ) a Jihar Sakkwato.

Sannan ta taba zama Mataimakiya ta musamman kan sabbin kafafen zamani, kafin daga bisani aka ba ta mukamin hadima kan ilimi.

Ta rasu ta bar ’ya’ya uku a duniya.