✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadarin motoci ya kashe mutum 19 a Katsina

Wani mummunan hadarin motoci ya sanadiyyar mutuwar mutum 19 da raunata wasu da dama a hanyar Funtuwa zuwa Zariya da ke cikin jihar Katsina. Majiyarmu…

Wani mummunan hadarin motoci ya sanadiyyar mutuwar mutum 19 da raunata wasu da dama a hanyar Funtuwa zuwa Zariya da ke cikin jihar Katsina.

Majiyarmu ta samu rahoton cewa hadarin ya faru ne a daidai Marabar Maska da misalin karfe 8 na dare ranar Lahadi, wanda ya rutsa tirela da wata motar fasinja kirar Volkswagen Sharon sannan sai kuma wata motar bas mai kujeru 18.

Wani ganau ya ce, tankar tirelar ce ta kauce hanya ta afka kan motar Volkswagen Sharon wacce take cike da fasinja sannan motar bas din tazo suka hadu.

Ya ce, ya kirga gawarwaki 19 yayin da wasu dama suka samu raunuka kuma an wuce da su asibiti.