Mutum hudu sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu biyar suka jikkata sakamakon hadarin mota da ya auku a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a ranar Litinin.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa a Jihar Ogun, Ahmed Umar, shi ne ya tabbatar wa manema labarai faruwar hakan a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.
- LABARAN AMINIYA: Zabar Sanata Kashim Shettima Abokin Takaran Tinubu Ya Dace – Zulum
- Za mu shiga yajin aikin nuna goyon baya ga ASUU – Ma’aikatan man fetur
Umar ya bayyana cewa, hadarin wanda ya rutsa da wata mota kirar Toyota Sienna da kuma wata babbar motar daukar kaya, ya auku ne da misalin karfe 3:22 na rana.
Ya ce gudun wuce sa’a da direban Sienna ya ke yi ne ya yi sanadiyar kwacewar motar kuma mummunan tsautsayin ya auku.
Jami’in ya ce, “Mutum tara ne hadarin ya rutsa da su, shida maza da mata biyu sai kuma karamin yaro daya. Hudu sun mutu, sannan biyar sun jikkata.”
Ya kara a cewa, an kwashi mutum biyar din da suka ji rauni zuwa wani asibiti da ke yankin Ogere don yi musu magani, yayin da aka kwashi wadanda suka mutun zuwa dakin adana gawarwaki na Babban Asibitin FOS a Ipara.
Kazalika, ya gargadi masu ababen hawa da su guji gudun wuce ka’ida musamman kuma a wannan lokaci na damina.
(NAN)