Mutum uku ne suka rasu yayin da hudu suka jikkata a wani hadari da ya auku a Kauyen Gunu da ke Karamar Hukumar Munya ta Jihar Neja.
Kwamandan Hukumar FRSC mai Kiyaye Hadurra ta Kasa reshen jihar, Mista Kumar Tsukam ne ya tabbatar da hakan yayin ganawa da Kamfanin Dillancin Labari na Kasa (NAN) ranar Lahadi a Minna, babban binrin jihar.
- Gwamnati za ta rage kashi 30 na cunkuso a gidajen gyaran hali
- Yadda ta kaya a manyan wasannin karshen mako a Firimiyar Ingila
A cewar Mista Tsukam, hadarin ya rutsa ne da motar haya da kuma wata karamar motar gida.
Kwamandan ya ce, “Hadarin ya rutsa da mutane bakwai, uku sun mutu hudu kuma sun jikkata.
Ya kara da cewa, “iyalan mamatan sun dauki gawarwakin su. An kuma mika motocin ga sashen binciken na ofishin ’yan sanda a Munya.
Tsakum ya yi zargin cewa hadarin ya faru ne a sakamakon gudun wuce sa’a da rashin kiyaye ka’idodin tuki.
Kazalika, ya bayyana cewa akwai rashin kula daga bangaren daya daga cikin direbobin.
Ya ba wa matafiya shawarar kula da ka’idodin tuki saboda guje wa aukuwar makamancin wannan tsautsayi.