✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hadarin mota ya kashe mutum 9 a Enugu

Akalla mutum tara ne suka rasu yayin da mutum 12 suka samu raunuka a hadarin mota a hanyar Enugu zuwa Fatakwal da ke karamar hukumar…

Akalla mutum tara ne suka rasu yayin da mutum 12 suka samu raunuka a hadarin mota a hanyar Enugu zuwa Fatakwal da ke karamar hukumar Awgu jihar Enugu.

Jami’in hulda na hukumar ‘yan sandan jihar Enugu SP Ebere Amaraizu ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai NAN hakan yau Lititin.

Amaraizu ya ce, lamarin ya faru ne a daren Lahadi, inda wata mota xauke da motar katapila suka hadu motar fasinjoji kirar bas.