Daga Hudubar Imam Muhammad Murtada Gusau
Masallacin Nagazi-Ubete, Okene Jihar Kogi
’Yan uwana! Wannan mutum bai yi imani cewa Allah Yana da ikon tayar da shi Ya yi masa hisabi ba, wanda hakan aiki ne na kafirci a fili balo-balo a bisa haduwar malaman Musulunci. Amma duk da haka Allah Ya gafarta masa wannan aiki na kafirci saboda gaskiyar jahilcin mutumin. Hakikanin jin tsoron Allah bisa irin imaninsa ya fi aikinsa na kafirci.
Ibn Taimiyya ya yi sharhi kan wannan Hadisi inda ya ce: “Allah Ya gafarta masa. Mutumin ya yi shakka a kan ikon Allah na iya tayar da shi idan ya zamo toka ko kura. Ya yi imani cewa Allah ba zai iya tayar da shi ba, wannan kuwa kafirci ne a bisa haduwar Musulmi, to amma ya yi hakan ne bisa jahilci. Bai san cewa zai iya yin haka ba, shi Musulmi ne da yake jin tsoron Allah zai yi masa ukuba don haka ne sai Allah Ya gafarta masa wannan.” (Majmu’ul Fatwa, mujalladi na 3 shafi na 231).
Kamar haka Ibn kayyim ya ce: “Idan aka karyata daya daga cikin wadannan mas’aloli na imani bisa jahilci ko gurguwar fassara ko tawili, ana iya yin uzuri kuma wanda ya yi haka ba za a kafirta shi ba, kamar yadda ya bayyana a wannan Hadisi inda mutumin ya musanta ikon Allah kuma ya umarci mutanensa su kone shi su watsa tokarsa a saman teku. Duk da wannan kuskure Allah Ya gafarta masa Ya yi masa rahama saboda jahilicinsa. Ilimi game da ikon Allah da ya riske shi ba ya musanta shi ba ne saboda girman kai ko niyyar ya yi karya.” (Madariji As- Salikin, mujalladi na 1 shafi na 347).
Don haka bai dace mu ayyana wani Musulmi mu ce shi ba Musulmi ba ne saboda ya aikata wani aiki na kafirci, balle kafirta daukacin al’ummar Musulmi. Za a iya daukar Musulmi ya kafirta ne idan shi da kansa ya bayyana cewa ya kafirta. Amma bayyana cewa sun yi imani abu ne da ya fi muhimmanci kuma tilas a yi aiki da shi wajen kare rayukansu kamar yadda shari’a ta gindaya.
At- Tahawi ya fadi a cikin muhimmin littafinsa kan akidar Ahlus Sunnah Wal Jama’a cewa: “Mutum ba ya rabuwa da addini face ya musanta abin da ya kawo shi cikinsa.” A duba Akida At-Tahawiyya.
Sannan As-Shaukani ya ce: “A sani game da hukuncin cewa wani Musulmi ya bar Musulunci ya koma kafiri ba abu ne mai sauki ga Musulmin da ya yi imani da Allah da Ranar Lahira ya ayyana shi ga wani ba, face akwai hujja da ta fi hasken rana bayyana.” A duba Sailul Jarar, mujalladi na 1 shafi na 978.
Saboda haka ne magabanta kwarai suke gudun fitarwa ko kafirta karkatattun da suka saba musu, domin hakkin Allah ne Shi kadai Ya yanke hukuncin wani Musulmi ya kafirta.
Ibn Taimiyya ya ce: “Malamai da ma’abuta Sunnah ba su kora ko kafirta wadanda suka saba musu koda wadanda suka saba musun sun kira su kafirai ba. Domin mas’alar kafirta hukunci ne na shari’a kuma ba za a yi ukuba wa mutum da irin haka ba, don haka idan wani ya yi maka karya ko ya yi zina da matarka bai halatta kai ka yi masa karya ko ka yi zina da iyalinsa ba. Zina da karya haramun ne a wurin Allah. Amma fitar da mutum daga Musulunci hakki ne na Allah Shi kadai. Don haka kada ku kafirta wasu face wadanda Allah da ManzonSa (SAW) suka ayyana cewa su kafirai ne.” A duba Ar-raddu ala Al-Bakri, mujalladi na 1 shafi na 381.
Wani babban abin koyi gare mu, shi ne Imam Ahmad bin Hambali (Rahimahullah), wanda ya yi tsaye yana adawa da kisa ko daure Mu’utazilawa. Masu guluwi a cikin Mu’utazilawa sun kirkiri cewa “Alkur’ani halitta ne,” kuma suna fitowa suna kafirtawa ko su ce duk wanda ya saba wa fahimtarsu, azzalumi ne. Sun kama Imam Ahmad sun kulle a kurkuku suka rika yi masa bulala, amma duk da haka ya ki kafirta su, ya ki a kafirta su, ya ki a la’ance su ko kiransu ’yan ta’adda. Maimakon haka Imam Ahmad ya fahimci cewa sun karkace ne saboda tawili, sai ya roki Allah Ya shiryar da su kuma Ya gafarta musu.
Ibn Taimiyya ya ce: “Imam Ahmad (Rahimahullah) ya yi addu’ar rahama da shiriya neman gafara ga wadanda suka uzzura masa (daga Mu’utazilawa) ne saboda ya san ba su fahimci cewa suna musanta Manzon Allah (SAW) ba ne, tare da karyata abin da ya zo da shi. Maimakon haka sun yi kuskure tare da koyi da bin wasu da suka gaya musu haka.” (Majmu Al Fatwa, mujalladi na 23 shafi na 349).
Wannan babban abin misali ne na hakuri da danne zuciya da tausayi na Imam Ahmad, sabanin ’yan tawaye masu tayar da zaune-tsaye da masu kafirta Musulmi a yau.
Ibn Taimiyya ma ya bi sawun Imam Ahmad wanda ya dauki mataki mai karfi na adawa da masu kafirtarwa.
Ibn Taimiyya ya ce: Wadanda ke zama da ni a koyaushe sun san ni mutum ne mai haramta a ce da wani mutum ya yi ridda ko ya kafirta ko shi mai zunubi, har sai in shari’a ce ta tabbatar da hujja cewa shi ba Musulmi ba ne. Kuma na tabbatar Allah Yana iya gafarta wa wannan al’umma kura-kuranta, ya alla kuskure ne wajen fassara ko aiki. Magabatan kwarai sun yi ta muhawara kan da dama kan wadannan ala’mura kuma babu wani daga cikinsu da ya ce da daya daga cikinsu ba Musulmi ba ne ko shi mai zunubi ne.” (Majmu Al Fatawa, mujalladi 3 shafi na 229).
Kuma duk da musgunawar da ya rika gani daga malaman da suke da sabani da shi, Ibn Taimiyya ya ki yarda ya fitar da wani Musulmi daga Musulunci.
Azzahabi ya ce: “Ibn Taimiyya ya fadi a karshen rayuwarsa cewa: “Ba zan ayyana wani daga cikin wannan al’umma a matsayin wanda ya kafirta ba.” (Siyar A’alam an Nubla, mujalladi na 15 shafi na 88).
A bisa wannan hali akwai bukatar mu dauki matakin a kan masu kafirta mutane da masu amfani da tarzoma da zubar da jinin al’ummar Musulmi. Wajibi ne mu fadi kuru-kuru cewa ayyana imani ga wani da kuma neman sulhu da zaman lafiya daga wani abu ne da ya wajaba a dauke shi da muhimmanci, kuma a tabbatar wannan sulhun zaman lafiya da aka gabatar ya taimaka nan take wajen hana tashin hankali.
A karshe, Annabi (SAW) ya ce: “Kashedinku, kada ku zamo kafirai a bayana, kuna karkashe junanku.” Buhari, Hadisi na 121.
Ya Allah! Ka sanya mu daga cikin wadanda suke samun gafararKa, kuma suke kubuta daga azabar wuta.
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a kan Shugabanmu Annabi Muhammadu (SAW) da alayensa da sahabbansa.
Nasara daga Allah take, kuma Allah ne Mafi sanin abin da ya fi dacewa.
Imam Murtada Muhammad Gusau, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Nagazi-Ubete da ke Okene a Jihar Kogi, ya gabatar da wannan Huduba ce a ranar Juma’a 11 ga Rabi’us Sani shekarar 1437 Bayan Hijira daidai da 22 ga Janairu, 2016. Za a iya tuntubarsa ta lambar waya: 08038289761