A ranar Litini da ta gabata ce al’ummar garin Jos fadar Jihar Filato suka shiga jimami da rudewa sakamakon rushewar wani bene mai hawa uku a Layin Butcher, Dilimi wanda ya yi sanadin rasuwar mutum 14.
Cikin wadanda suka rasu a hadari har da mai gidan wanda fitataccen dan kasuwa ne, mai harkokin sayar da magunguna a garin Jos, mai suna Alhaji Kabiru Lawal Nalele.
Da yake yi wa Aminiya bayani kan yadda abin ya faru da yadda ya kubuta a wannan hadari, daya daga cikin ’ya’yan Alhaji Kabiru Nalele, mai suna Khamis Kabir mai shekara 17, ya ce lokacin da wannan abu ya faru suna tare da Babansa a shagon sayar da magani na yayarsa Amina da ke gidan.
Ya ce lokacin da wannan abu ya faru, ba su ji karar komai ba, sai suka ga shagon da suke ciki yana ta tsagewa a daidai lokacin da masu aiki suke kokarin cire gilashin wata kofa a gidan.
Ya ce kafin su fita, sai ya ji wani gini ya danne shi tare da Babansa da kuma yayar tasa.
“Lokacin da wannan abu ya faru, ina cikin hayyacina don haka na yi ta yin ihu ina cewa Baba ku tashi ga mutane nan, sun zo za a bude mu. Lokacin da muke kwance an kira wayar Babanmu tana ta kara, shi kuma gini ya danne masa kai, shi ne sai na matsa da hannuna na daga wayar. Sai aka ce mini ina nake? Na ce ni bai san inda nake ba,” inji shi.
Ya kara da cewa: “Sai na ga an taba wani waje sai na ga kujera ta fado, na ce ina ganin kujera shi ne sai aka hasko mini fitila, aka ce in turo wani abu. Ina kwance sai na janyo wata sanda na tura shi ne aka ce an gan ni, shi ne aka faso wurin aka ciro ni. Na ce a kyale ni a ciro Babana da Yayata tukuna, shi ne suka ciro ni aka tafi da ni asibiti.”
Da take yi wa Aminiya bayani kan yadda lamarin ya faru, wata makwabciyar gidan mai suna Maryam Aminu Bako, ta ce wannan abin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar.
Ta ce tana tsaye ta tagar gidansu, sai kawai ta ji wata irin kara a gidan. Sai ta ga ginin binen ya sauka kasa. Ta ce nan take sai jama’a ta ko’ina suka rugo domin ceto rayukan wadanda suke cikin gidan.
Maryam Bako ta ce kasan gida shagon sayar da magani ne. Saman gidan kuma dan mai gidan ne yake zaune da iyalansa.
Da yake zantawa da wakilinmu kan lamarin kaein mai gidan kuma Mataimakin Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa ta Karamar Hukumar Jos ta Arewa, Alhaji Habibu Lawal Nalele, ya ce dan uwan nasa babban dan kasuwa ne da yake harkokin sayar da magunguna a garin Jos.
Ya ce kamfaninsa na sayar da magunguna yana da rassa da ma’aikata maza da mata sama da 30 a garin Jos.
Habibu Nalele ya ce lokacin da ya isa gidan mai hawa uku bayan ya samu labarin abin da ya faru, sai ya samu ya rushe kasa baki daya. Kuma ya samu dubban mutane sun taru suna ta kokarin ceto rayukan wadanda suke ciki.
Ya ce an samu an ciro gawar dan uwansa marigayi Alhaji Kabir daga ginin da misalin karfe 9:00 na dare tare da ’yarsa Amina da kuma jikansa. Domin lokacin da wannan abu ya faru, suna cikin shagon sayar da maganin na Amina da ke gidan. Kuma Amina tana da ciki bayan wannan yaro nata.
Haka kuma ya ce akwai Safiya wadda ita ma ’yarsa ce da Rukayya ’yar wansu da Maryam ’yar uwar mijin Amina da yara kanana uku duk sun rasu a gidan.
Ya ce sannan akwai wani mai walda wanda ya zo ya yiwa Alhajin aiki shi ma ya rasu a hadarin.
Alhaji Habibu Nalele ya ce abin da labari ya zo musu shi ne akwai wajen da ya tsage a gidan. Shi ne Alhaji Kabiru ya dauko mai gyara da niyyar ya gyara wata kofa. Suna cikin aikin gyaran kofar ce, sai wannan lamari ya faru.
Ya ce Alhaji Kabiru ya je gidan ne da niyyar za a yi masa gyara a gidan, amma ba a cikin gidan yake zaune da iyalansa ba.Ya ce dansa Rufa’i ne yake zaune a gidan tare da iyalansa amma lokacin da abin ya faru Rufa’in ba ya gidan.
Dangane da maganganun da ake yi cewa asalin gida na wanka ne, Habibu Nalele ya ce babu shakka akwai bayan gida da wajen wanka a gidan kuma an tona rijiyar burtsatse a waje. Amma dai gidan gini ne aka yi, domin a da tsohon gini ne marigayin ya rushe shi, ya yi sabon gini. Don haka sun dauki wannan al’amari a matsayin kaddara sun bar wa Allah.
Ya ce ’ya’yan Alhaji Kabiru da suka rasu a hadari su ne Amina da Safiya da jikokinsa uku da ’yar babban wansu Rukayya da Maryam ’yan uwar mijin Amina da kuma amaryar dansa Rufa’i. Ya ce mutum 4 ne suka tsira a hadarin da suka hada da matar dansa Abdurrahaman da danta da dansa Khamis da wani mai sayen kaya. Ya ce marigayin ya rasu ya bar mata 4 da ’ya’ya sama da 20.
Alhaji Habibu Nalele ya mika godiya ga ’yan sanda da sojoji da jami’an kashe gobara da ’yan sintiri da kungiyoyin sa-kai da al’ummar garin Jos baki daya kan kokarin da suka yi wajen ganin an ceto rayukan wadannan bayin Allah.
Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa [NEMA] ta tabbatar da cewa mutum 12 ne suka rasu kafin wadansu biyu su sake rasuwa daga baya.
Babban Limamin Jos, Sheikh Lawal Adam ne ya jagoranci Sallar Jana’izar wadanda suka rasu, inda aka binne su a babbar makabartar da ke hanyar Zariya a Jos, a safiyar Talata.
Da yake zantawa da Aminiya kan wannan lamari Shugaban Sashin Bincike da Ceto na Hukumar NEMA a yankin Arewa ta Tsakiya, Nurudeen Musa ya ce mutum 12 ne suka rasu a hadarin, yayin da mutum 4 suka tsira da raunuka.
Ya ce a karshen aikin ceton da suka gudanar wanda suka fara tun yammacin ranar Litinin, zuwa wayewar garin Talata sun gano gawar mutum na karshe, mai suna Mubarak wanda shi ne aka dauko, don yin aikin walda a gidan, lokacin da hadarin ya faru.
Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya jajanta wa iyalan wadanda hadarin ya rutsa da su, lokacin da ya ziyarci wurin da hadarin ya faru.
Ya ce akwai abin da Allah Yake kawowa kuma akwai abin da mutane suke jawo wa kansu. Ya ce don haka ya kamata jama’a su rika lura idan za su yi gini su tabbatar sun samu izini daga Hukumar Raya Garin Jos da Kewaye (JMDB), ko Ma’aikatar Kasa da Safiyo ta Jihar Filato don kauce wa yin gini marar kwari.
Ya ce idan aka samu izini daga wadannan hukumomi a tabbatar an samu wadanda za su kula da ginin, domin su sa ido a yi ginin yadda ya kamata.
Gwamnan wanda Mataimakinsa Farfesa Sonni Gwanle Tyoden ya wakilta, ya ce daga yanzu jami’an Hukumar JMDB za su rika bi layi-layi a garin Jos, domin su ga gidajen da suka kusa rushewa su rika sanya lambobi a gidajen domin a rushe su. “Ba son gwamnati ne a rushe gidan kowa ba, amma ya kamata mu taru mu rage wa kanmu asarar rai, domin asarar rai ta fi kowace asara,” inji shi.
Shi ma dan takarar Gwamnan Jihar Filato karkashin Jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata Sanata Jeremiah Useni ya kai ziyarar jajanta wa iyalan wadanda hadarin ya rutsa da su.