✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadakar jam’iyyun kasar Habasha sun zabi Dokta Ahmed ya zama Firayi Minista

Bayan kwana da kwanaki ana zazzafar muhawara da yarjejeniya a kasar Habasha, shugabannin hadakar jam’iyyun da ke mulki a Habasha, sun zabi Dokta Abiy Ahmed…

Bayan kwana da kwanaki ana zazzafar muhawara da yarjejeniya a kasar Habasha, shugabannin hadakar jam’iyyun da ke mulki a Habasha, sun zabi Dokta Abiy Ahmed ya zama sabon shugaban hadakar, wanda hakan zai sa ya zama sabon Firayi Ministan kasar.

Kafar Labarai ta BBC ta rairayo tarihin Abiy Ahmed, inda ta ce an haife shi a ranar 15 ga Agustan 1976, kuma ya fito ne daga kabilar Oromo mai rinjayen jama’a, wadda take kan gaba wajen shiryawa da jagorantar zanga-zangar hamayya da gwamnati tun shekarar 2015.

Ya taso ne a iyalin da suke da al’ada da kuma addini daban-daban, inda mahaifinsa, Ahmed Ali ya kasance Musulmi dan kabilar Oromo yayin da mahaifiyarsa ta kasance Kirista.

A lokacin da yake matashi a 991 ya shiga gwagwarmayar amfani da makamai da yaki da gwamnatin Gurguzu ta kasar a lokacin.

Kuma ya kasance daya daga cikin sojojin hadaka da suka yi sanadiyyar faduwar gwamnatin Gurguzun a 1991.

Bayan faduwar gwamnatin ne a wancan lokacin ya samu cikakken horon zama soja, kuma ya zama sojan kasar ta Habasha, a fannin tattara bayanan sirri da kuma sadarwa.

A lokacin da yake sojan ne Abiy ya yi karatun digirinsa na farko a fannin ilimin injiniyan kwamfuta a Kwalejin Microlink Information Technology da ke Addis Ababa a shekarar 2001.

Ana kallon Dokta Ahmed a matsayin wani gwarzon dan siyasa wanda yake da kwarewa a fannin boko da kuma soji.

Yana da takardar shaidar digirin-digirgir daga Jami’ar Addis Ababa, kuma ya yi digiri na biyu a Amurka da kuma Birtaniya.

A baya ya taba rike mukamin Minista a kasar Habasha, kuma shi ne ya taimaka wajen kafa Hukumar Leken Asiri ta kasar.

Sai dai kuma masu sukar lamirinsa suna ganin abu ne mai wuya a ba shi isasshiyar dama da kuma ikon kawo sauye-sauyen da masu zanga-zangar hamayya da gwamnatin ke bukata.

daruruwan mutane sun rasa rayukansu sannan an tsare da dama tun lokacin da aka fara zanga-zanga a kasar kusan shekara uku da ta wuce.