✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Haɗa kan Arewa da samar wa yankin mafita a siyasa ne manufarmu — Shekarau

Ana ta surutun cewa Arewa ta lalace, matasa sun lalace, ba shugabannin kirki, ana ta sace kuɗaɗen al’umma.

Wata sabuwar ƙungiya ta wasu ’yan siyasa a Arewa, ta ce ta fara shirin samar da mafita ga yankin.

Wasu da suke kiran kansu da masu kishin Arewa sun ɓullo da sabon yunƙurin ne da nufin sama wa yankin ingantaccen shugabanci da alƙibla ta fuskar siyasa da tattalin arziki da zamantakewa.

Sun kira wannan ƙungiya tasu da League of Northern Democrats a Turance.

A taron da wasu masu faɗa- a-ji na Arewa suka gudanar a ranar Talata a Abuja, taron ya haɗo tsofaffin gwamnoni da ma’aikatan gwamnati da ’yan siyasa da tsofaffin sojoji da ’yan sanda da sauransu.

A taron an amince da naɗa tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Ministan Ilimi Malam Ibrahim Shekarau a matsayin jagora.

Mahalarta taron sun ce sun yi la’akari da zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi wadda ta ƙara nuna wa duniya irin girman ƙalubalen da Arewa ke fuskanta.

Malam Ibrahim Shekarau ya ce, matsalolin Arewa sai ƙara haɓaka suke yi, don haka dole a zauna a nemi mafita.

Ya ce, “Ana ta surutun cewa Arewa ta lalace, matasa sun lalace, ba shugabannin kirki, ana ta sace kuɗaɗen al’umma, shi ya  sa muka zaƙulo masana, gogaggu a fannoni daban-daban mu kusan 200, don samun mashala.”

“Babbar manufarmu ita ce, waɗanne matakai za mu ɗauka don faɗakar da al’ummar Arewa game da mutanen da ya kamata su shugabance su,” in ji Shekarau.

Hajiya Inna Maryam Chiroma, tsohuwar Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP ta Ƙasa ta ce halin da ake ciki aArewa, abin a tsaya a duba ne, don a kawo gyaran da ya dace.

Amma wasu masu sharhi sun bayyana wannan yunƙuri na ƙoƙarin farfaɗo da Arewa a matsayin wata manufar siyasa, kuma ƙungiyar na iya rikiɗewa ta koma wata jam’iyyar siyasa idan tafiya ta yi nisa, musamman bisa la’akari da rarrabuwar kan shugabannin yankin Arewa.