✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gyaran Najeriya ba na Buhari kadai ba ne – Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce gyaran Najeriya ba na Shugaban kasa Muhammadu Buhari shi kadai ba ne. Atiku Abubakar ya bayyana haka…

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce gyaran Najeriya ba na Shugaban kasa Muhammadu Buhari shi kadai ba ne. Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a sakonsa na Ranar Ma’aikata ta bana, inda Turakin na Adamawa ya ce idan aka lura da dimbin kalubalen da kasar nan da mutanenta ke fuskanta akwai bukatar kowa ya tallafa wa kokarin gwamnatin Buhari na fitar da jaki daga duma.
Atiku ya ce: “Shugaba Buhari kadai ba zai gyara Najeriya ba. Akwai bukatar kowa da kowa – zababbbu da nadaddun jami’ai da ’yan majalisa da bangaren shari’a da ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu da talakawan Najeriya – su yi aiki tare cikin imani da sadaukarwa domin kawo canjin da ake bukata.”
Ya kara da cewa: “Lura da karancin kudin shigar da ake samu daga man fetur, ya zama wajibi a kanmu mu hada hannu wajen samo mafita, kuma hakan zai samu ne ta hanyar kara bullo da dabaru daga bangaren gwamnati da kuma kara kwazo daga bangaren jama’a.”
Atiku Abubakar ya kuma ce: “Akwai bukatar dukkanmu mu sadaukar da kai, bisa lura da hakikanin halin da ake ciki. Bai dace ba a nemi ma’aikata su sadaukar da kai a yayin da manyan masu rike da mukamai suke ci gaba da shan lagwada, irin wannan hali zai iya jawo rashin jin dadi a wuraren gudanar da aiki.” Ya ce abu ne mai wuya a gamsar da ma’aikata kan su sadaukar da kai a yayin da manyan masu rike da mukamai suke gudanar da rayuwar da ta yi hannun riga da halin da tattalin arzikin kasa yake ciki.
Sai ya bukaci ma’aikatan Najeriya da kada su yanke kauna daga cewa wannan gwamnati ta Shugaba Buhari za ta iya magance wadannan matsaloli.
Wannan bayani na Atiku ya zo ne a daidai lokacin da kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta koka cewa ’yan Najeriya sun fara yanke kauna daga canjin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi musu alkawari. Shugaban kungiyar ta kasa Ayuba Wabba, ya bukaci Shugaba Buhari ya samar da tsare-tsare da dabaru na aiki da cikawa ban a romon baka ba.