✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gyaran kasa: Ta ina za’a fara?

Yanzu da aka zabi Janar Muhammadu Buhari a matsayin Shugaban kasa babban abin da jama’a suke fata shi ne batun gyaran kasa. Sai dai abin…

Yanzu da aka zabi Janar Muhammadu Buhari a matsayin Shugaban kasa babban abin da jama’a suke fata shi ne batun gyaran kasa. Sai dai abin tambaya ta ina za a fara gyaran. kasar nan akwai dimbin matsalolin da sai ka rasa ta ina za a fara gyara. Abin ban haushi da takaici a kasar nan shi ne a daidai lokacin da aka banzatar da ’yan fansho da suka yi shekara da shekaru da ritaya, kuma a daidai lokacin da aka rufe ko aka rusa kamfanoni da hukumomin Gwamnatin Tarayya da na jihohi, kamar Kamfanin Buga Jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo da Bankin Arewa (BON) da Masakar Kaduna (KTL) da sauran masaku da hukumomin jiragen kasa da na sama na Najeriya da sauransu, sai ga shi bincike ya nuna wasu ma’aikatan tarayya da jihohi suna ninka kudin fansho na tsofaffin ma’aikatan da suka yi ritaya sau uku ko fiye kuma duk su sace, ko su ajiye a bankuna ana ba su kudin ruwa. Hatta Turawan da suka yi mulkin mallaka duk da sun mutu, ana fitar da kudin da sunan biyansu fansho, alhali ga masu rai an ki biyansu suna mutuwa da yunwa. Abin ya gangaro wadanda suke yin aikin ma ba sa samun albashi a kan lokaci musamman kananan ma’aikata da su ne suka fi yawa inda sukan yi wata uku ko fiye ba albashi, bayan karancin albashin inda wasu ko mako biyu ba ya kai su.

Sannan ga wadanda suka gama karatu tsawon shekaru ba su samu aikin yi ba, ’yan makaranta ba su samun koyarwa saboda halin da malamai suke ciki na rashin albashi mai kyau. Kuma hakan ya hada har da jami’an tsaro-kananan sojoji da ’yan sanda da SSS da ire-irensu, har ta kai an daure Sufeto Janar na ’yan sanda bayan an kwato biliyoyin Naira daga hannunsa.
Yanzu an gano wasu sun yi rub-da-ciki a kan kusan Naira biliyan 160 na ’yan fansho, an ce ma’aikaci daya an samu tsabar Naira biliyan biyu a dakinsa. Wadannan abubuwa kullum karuwa suke yi tsawon shekaru amma an kasa magance su a gwamnatance.
Yanzu ne ya kamata mu fara tunanin yin gyara ba wai sai lokacin zabe ya zo wadanda aka zalunta su tare a gindin ’yan takara domin a ba su ashana da sabulu ko taliya da Naira 500, ko turmin atamfa ko shadda yadi biyar ba, don su zabi gungun azzalumai da ba a san asalinsu ba, wadanda bayan an zabe su sukan yi rub-da-ciki a kan amanar da aka danka musu.
Misali tsohon Gwamnan Jihar Delta Mista James Ibori da ya yi mulki tsakanin 1999 zuwa 2007 ya tafka wa jama’ar jiharsa sata, an yi ta kuka a kai, amma kotun Najeriya ta sanya sabulu ta wanke shi fes daga zarge-zarge fiye da 140. Amma Ingila inda ya kai kudin satar kan zarge-zargen da ba su fi 10 ba, ta daure shi shekara 13 kan laifin shiga kasarta da kudin da ya sato daga Najeriya ya kai can!
Ana cikin hayaniyar wannan lamari ne sai kwatsam! Majalisar Tarayya ta bankado an sace mana sama da Naira biliyan 1,400, (Naira tiriliyan daya da biliyan 400). Yanzu satar ma an daina yayin ta Naira biliyan sai tiriliyan. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!
Kamar yadda na fada a sashin Hausa na Muryar Amurka ranar Juma’a 20-4-2012 da karfe 6:00 na safe, sama da Naira tirilyan daya da Kwamitin Faruk Lawal ya bankado an sace mana da sunan tallafin mai bayan an sa mu mun yi ta biya da bala’in tsada da raba kudin za a yi ga daukacin jama’ar Najeriya da kowa zai samu Naira miliyan shida da kwata, har a samu rarar Naira biliyan 40 matukar ba mu fi mutum miliyan 160 a kasar nan ba. Nan ne ma na bayar da sahawarar a kafa wani kwamiti na amintattun mutane mai karfin shari’a da zai kwato mana wadannan kudade kasancewar kudin mai fetur ne da gas da kananzir da muka biya tilas dinmu. Wannan kwamiti ya zuba wannan kudi wajen kafa sababbin matatun mai guda shida kowace shiyya ta samu daya a kan Naira biliyan daya kowanne. Bayan haka sai a ba kowane dan Najeriya takardar mallakar hannun jari ta Naira miliyan shida da kwatar nan da na ambata. A karshen kowane wata uku ko shida a rika ba kowa ribar da ya samu, ta haka sai a huta da barace-barace da raraka da maula da ayyukan ta’addanci da ake kuka da su a yanzu.
Aikin wadanda ake zaba ne yanzu su kwato wa duk wanda aka zalunta hakkinsa daga hannun azzalumai. Kamar yadda majalisa ta fallasa, mun sanya ido bangaren zartarwa ya yi amfani da ikonsa wajen kwato wadannan kudade.
Wajibi ne a kan bangaren zartarwa a matakin karamar hukuma zuwa jiha da tarayya su tabbatar da tsaron rayuka da lafiya da dukiya da mutunci da addinin duk wani dan kasa ko bako.
Mu kuma talakawa a namu bangare mu yi kokarin canja irin makauniyar biyayya da tumasanci da muke yi wa shugabanni zababbu ko nadaddu.
Kuma ya kamata mu fahimci cewa a yanzu babu wata jam’iyyar siyasa ko wani zabe da zai canja yanayin da ake ciki, sai daidaikun mutane sun canja halayensu na saba wa Allah da zaluntar ’yan uwansu, sannan a hadu a sake sabon tsari na gaskiya tsakani da Allah.
Wani muhimmin abu shi ne yadda bangaranci ya yi tasiri a siyasar Najeriya fiye da komai, misali maganar shiyya-shiyya ba ta cikin tsarin mulkin Najeriya, amma ana fifita ta fiye da abin da ke cikin tsarin mulkin, wannan ya sa ko sata mutum ya yi kiri-kiri ba kunya ba tsoro, mutanen da ya fito daga yankinsu za su fito suna kare shi.
Akwai bukatar a kwato duk dukiya ko kadarorin da zababbu ko nadaddu da ma’aikata suka mallaka ba bisa ka’ida ba, ko suka yi wa kansu dokokin zaluntar talakawa suka mallake su, tun daga kananan hukumomi zuwa jihohi da tarayya. Kada a ce sai an kama mutum yana sata, da an ga abin da ya mallaka ya fi karfin samunsa a dauke shi a matsayin marar gaskiya, har sai ya tabbatar da yadda aka yi ya samu wannan dukiya. Yin haka shi ne a fahimtata zai magance rikice-rikicen kabilanci da na addini da tashin bama-bamai a wasu sassan Najeriya a huta da salwantar rayukan bayin Allah da ba su ji ba ba su gani ba. Kuma ta haka ne dimokuradiyyar da ake ta kururuwa a kai, za ta yi tasiri.
Alhaji Abdulkarim dayyabu,
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya,
Kano.
08023106666, 08173106666, 064983333.
Imel:[email protected]