Tunda Gwamnatin Jihar Kaduna ta saki sakamakon jarrabawar gane cancantar ilmin malaman makarantun Firamaren jihar da ta gudanar a cikin watan Yunin da ya gabata, ake ta samun ce-ce-ku-ce, har ma da fito-na-fito irin ta zanga-zangar nuna kin jinin aniyar da gwamnatin ta dauka na ganin ta sallami dukkan malaman makarantun Firamaren da ba su ci jarrabawar ba, cikin masu zanga-zangar akwai kungiyoyin kwadago karkashin jagorancin hadaddiyar kungiyar kwadago ta kasa, wato NLC da na dalibai.
Sakamakon wancan jarrabawar ya tabbatar da cewa daga cikin malaman makarantun Firamaren jihar dubu 33, da su ka zauna jarrabawar malamai 11,220, kadai su ka ci jarrabawar, yayinda 21,780, suka fadi jarrabawar da aka sa makin cinta akan 75, cikin 100, sabanin maki 40, da aka sa ni a kan cin kowacce irin jarrabawa ta karatun boko. Wasu daga cikin tambayoyin da aka yi a kan jarrabawar da Gwamnatin Jihar Kadunan, ta ce daidai ta ke da ta ilmin da aji hudu na makarantar Firamare, sun hada da fannin ilmin koyasrwa da ya kamata dukkan wanda zai koyas yana da shi, kamar yadda Gwamnan Jihar Malam Nasir El-Rufa’I ya bayyana wasun su a shafinsa na Tiwita kamar haka:- (a) Ya ya za ka koyar da dalibi darasi? (b) Muhimman abubuwa biyu a kan bukatar lallai da za su sa malami ya rinka shirya tsarin koyarwarsa? (c) Bayyana abubuwa biyu muhimmai da suke taimaka wa koyarwa? (d) Bayyana wasu muhimman abubuwa biyu na bangaran shirya darasi.
Tambayoyin da suka fado a kan rubuta bayani a takaice sun hada da :- (a) Kawo wasu laifuffuka biyu da suka shafi yin ta’annati da kudaden jama’a? (b) Me Hukumar yaki da ta’annati da kudaden jama’a, wato EFCC take yi? (c) Me ke aikin Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC? (d) A takaice bayyana ayyukan kotun da’ar ma’aikata ta CCB. Duba da irin yadda aka shirya waccan jarrabawar, mai karatu za ka iya cewa ta yi tsauri ga dan aji hudun makarantun Firamare na gwamnatoci, sai dai ga daliban Firamare na makarantun kudi na ‘ya ‘yan masu hannu da shuni ko masu rike da madafan iko irin su Gwamna El-Rufa’i. Amma ba ta yi tsauri ko kadan ba ga dukkan wanda ya amsa sunan ya yi karatun koyarwa a kasar nan. Don haka sanya makin cin jarrabawar akan maki 75 cikin 100, ko kusa bai kamata ya zama wani abin ce-ce-ku-ce.
Aniyar da gwamna El-Rufa’i ya dauka na ganin ba gudu ba ja da baya sai ya sallami dukkan malamin da bai ci waccan jarrabawa ba, da aniyar ma ye shi da wanda ya cancanta, wani abin a yaba wa gwamnan ne, sannan kuma a kama masa a kan dukkan hanyoyin da zai bi ya ci nasara. Don kuwa sanin kowa ne a kasar nan cewa harkar daukar ma’aikata aiki ko wane iri musamman na gwamnati ya zama a kan alfarma ba cancanta ba. Haka labarin yake a wajen daukar malaman makarantu a kan aikin koyarwa, musamman a cikin majalisun kananan hukumomin kasar nan wadanda suke da alhakin hakan. Hakan ya sanya aka mayar da daukar malaman makarantun Firamare ko har ma da na ga ba da Firamare a kan siyasa ba cancanta ba. Tunda aka dawo wannan mulkin na dimokuradiyya a shekarar 1999. Don haka ina laifin Gwamna El-Rufa’i da ya yi ta maza ya tunkari gyaran wannan muhimmin fannin ilmi na tun daga tushe, ta hanyar sallamar dukkan malamin da bai cancanta ba.
Amma da yake mulkin dimokuradiyya da ke ba da damar ‘yancin fadin albarkacin baki ko da kuwa ba don yadda za a gyara ba, ta sanya hadaddiyar kungiyar kwadago ta kasa wato NLC da wasu dalibai a bisa gayyatar kungiyar malaman makarantu ta NUT reshen Jihar Kaduna suka gudanar da wata zanga-zanga a Kadunar a ranar Larabar makon jiya. A yayin wancen zanga-zangar da shugaban kungiyar kwadago ta NLC na kasa baki daya Kwamared Ayuba Wabba ya shugabanta an ji shi yana shan alwashin cewa muddin Gwamna El-Rufa’i bai janye aniyarsa ta korar wadancan malamai sama da dubu 21 ba, don maye gurbinsu da wasu to kuwa kungiyoyin kwadagon sun sha alwashin dakatar da dukkan harkokin yau da kullum a Jihar Kaduna, kamar rufe filin jirgin sama da tashar jirgin kasa da kasuwanni da ma’aikatu da dukkan makarantu da sauran guraren hada-hadar jama’a a dukkan fadin jihar.
Hanzarin Kwamared Wabba shi ne babban laifi ne a sallami ma’aikaci haka suddan daga bakin aikinsa kuma hakan na iya kara kawo rashin ayyukan yi da kuma jefa wadanda korar ka iya shafa cikin aikata miyagun laifuka. Bayan waccen zanga-zangar ‘yan kwadagon ta Kaduna, wadda har ta kai ‘yan kwadagon sun farfasa gilasan ginin Majalisar Dokoki ta Kaduna, barnar da gwamnatin jihar ta ce ko kusa ba za ta lamunta ba, kamar yadda Babban Sakatare na ma’aikatar ilmi na jihar Alhaji Adamu Mansur ya mayar da martani a madadin gwamnan jihar, jim kadan bayan waccan zanga-zanga, gwamnati na nan ta shirya tsaf da cikakkun shaidu da za ta gurfanar da wadanda suka yi waccan ta’addanci gaban kuliya.
Shi ma Sanata Shehu Sani mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa da aka dade ana jin hargowarsa ta sukar dukkan aikace-aikacen Gwamnatin Gwamna El-Rufa’i, a kan wannan batu ma an ji shi yana fada wa taron manema labarai cewa aniyar gwamnan na ya sallami malaman makarantun Firamare shi ne kokuwar hauka, sannan kuma gwmanan yana son ya maye gurbinsu da na shi magoya bayan. Haba Sanata Sani! Idan shugaban kungiyar kwadago na kasa baki daya daga baya ya yi zargin cewa, ‘wadanda suka fadi jarrabawar wasunsu masu gadi da leburori, sannan kuma wasu sunayen da aka ce sun ci jarrabawar malamai ne da wala Allah sukai ritaya ko su ka mutu.
Ya ci ace Sanata Shehu Sani bai sanya siyasa ba a cikin wannan muhimmin al’amari da ake neman a ceto makomar daliban Firamare sama da miliyan 2, da a yau suke cikin makarantun Firamaren jihar baya ga wadanda za su biyo baya a gobe in Allah Ya nuna mana.
Ni, a nawa haukan irin yadda nasan Sanata Sani dan gwagwarmaya mayakin ‘yancin bil adama, musamman talakawa tun kafin ya je Majalisa ya ci a ce ya mara wa Gwamna El-Rufa’i a wannan kyaykkyawar aniya ta shi ta ceto fannin ilmi a jiharsa ta Kaduna wajen gabatar da kudurin a zauren Majalisa da zai nemi dukkan gwamnonin Arewa 19, musamman na shiyyar da ya fito ta Arewa maso Yamma da su yi koyi da abin da gwamnansa na Kaduna ya yi, don kuwa a yanzu dukkan makarantun wadannan jihohi cike suke da rubabbun malaman makarantun Firamare kai har ma da na Sakandare.
Tabbas, ina fadi ina kara fadi cewa ina tare da Gwamna El-Rufa’i a kan wannan aniya da ya sa gaba da fatan sauran takwarorinsa na Arewa za su yi koyi da shi. Ko kusa karsu ji tsoron kowace irin barazana daga kungiyoyin kwadago ko ‘yan hamayyar soki-burutsu. Ina fata kuma idan Gwamna El-Rufa’i ya ci nasara (wadda in Allah Ya so zai ci) sallamar malaman da ba su cancanta ba ya dauki wadanda suka cancanta, to kuma ya mayar da hankali wajen inganta jin dadin malaman makarantun, walau ta karin girma da horarwa akai-akai, da wadata makarantu da dukkan kayayyakin ayyukan koyo da koyarwa da suka kamata.