✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gyara fatarki da zuma

Zuma ta kasance babban maganin cuttuttuka da dama don haka ya kamata mu kula da ita. A yau mun kawo muku hanyoyin da za a…

Zuma ta kasance babban maganin cuttuttuka da dama don haka ya kamata mu kula da ita. A yau mun kawo muku hanyoyin da za a bi a magance cututtukan fata da zuma. Daga ciki akwai; kyasbi da kuraje da tabo da gyaran farce da sauransu. A sha karatu lafiya.

•Don magance kurajen fuska : Ana shafa zuma a kan kurajen da suka feso a kullum a kalla safe da yamma. Sannan sai a wanke da ruwan dumi bayan minti goma zuwa goma sha biyar za a ga canji.
•Tabo: Zuma na dauke da sinadaren haskaka fata idan ana shafa shi a kan tabo a kullum a hankali tabon zai zo ya bace.
•Farce: Zuma tana sanya farce kyau. Idan ana da farce mai tauri, za a iya a kwaba zuma da ruwan ‘benegar’ sannan a rika shafawa a farce sai a wanke bayan minti goma.
•kyasbi:A samu zuma mai kyau sai a rika shafawa a kan kyasbin na tsawon minti goma kafin a wanke. Yana da kyau a rika shafawa a kullum na tsawon watanni hudu ba tare da an huta koda na kwana daya ba.
•kurajen aski:Bayan an yi aski ko an aske gemu yana da kyau a shafa zuma a wajen da aka yi aski. A jira na tsawon mintuna goma zuwa sha biyar sannan a wanke. Idan ana hakan zai hana fesowar kuraje.
•Rage gashin jiki: Zuma tana rage gashin jiki. Idan aka hada zuma da ruwan lemon tsami da suga. Sannan sai a tafasa su har sai ruwan ya canza kala. Sannan a sauke a bari ya dan huce. A samu auduga a tsoma a hadin sannan a shafa a fatar jiki inda akwai gashi. Bayan ’yan mintuna kadan, sai a daga audugar. Hakan na cire gashin fatar jiki.
•kunar rana : Zuma na warkar da dabbare-dabbare bakake da ke fitowa a fuska. A shafa zuma a inda ake da matsala sannan a wanke bayan mintuna goma zuwa sha biyar. Yana da kyau a rika gwada irin wannan salon sau biyu a sati domin samun biyan bukata.