Gwamnonin Jihohin yankin Tafkin Chadi na taro a N’Djamena, babban birnin kasar Chadi domin nazarin bangarorin hadin gwiwa domin samar da zaman lafiya da ci gaba.
Hukumar Kula da Tafkin Chadi tare da hadin gwiwar Kungiyar Tarayyar Turai da shirin raya kasashe na Majalisar Dinkin Duniya da sauran abokan hulda ne suka shirya taron.
- Sojoji su harbe ’yan ta’addan da ke kokarin tsallakowa Najeriya daga Kamaru
- Bidiyon Dala: APC ta bukaci Ganduje ya yi watsi da sammacin Muhuyi
Taron wanda ke da taken: “Sabbin Dama don Zaman Lafiya a Tsarin Tsaro na Canji”, wani shiri na gaske don inganta tattaunawar yankin da kuma zana darussa kan kalubalen kasa da kasa kan harkokin tsaron da yankin ke fama da shi.
Har ila yau, wata dama ce ta daidaita ayyukan hadin gwiwa don samo mafita ga kalubalen da suka shafi yankunan da ke kewayen Tafkin.
Gwamnonin takwas da suka halarci taron na hudu ana sa ran za su karfafa ikon mallakar muhimman abubuwan da suka sa a gaba.
Abubuwan dasu sun hada da suka hada da yanayin tsaro da ke kunno kai a yankin da kuma tasirin kokarin da ake yi na kammala dawo da ikon jihohin a yankin.
Za kuma su yi nazari kan ci gaban da aka samu a cikin shekaru biyar da suka gabata, tare da gabatar da muhimman tsare-tsare a nan gaba.
Hakazalika gwamnonin za su yi nazari a kan harkokin noma da makiyaya, da kuma yadda al’umma za su iya jurewa da zaman lafiya a yankin tafkin Chadi.