Gwamnonin da aka zaba karkashin jam’iyyar PDP za su gana a ranar Laraba gabanin taron Kwamitin Zartarwa na jam’iyyar da aka tsara ranar 9 ga watan Satumba.
Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP, Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sakkwato, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Darakta-Janar na kungiyar, C.I.D Maduabum, ya fitar da sanyin safiyar Laraba a Abuja.
Sanarwar ta bayyana cewa Tambuwal ya tuntubi gwamnonin, inda suka kira wani taro na musamman da zai gudana a ranar Laraba da karfe 3 na yamma.
Taron, a cewar sanarwar, zai tattauna batutuwan da suka taso a jam’iyyar da kuma dabarun sake canza fasalinta kafin taron Kwamitin Zartarwa da za a yi ranar Alhamis.
Ya sake tabbatar wa dukkan mambobi da masu ruwa da tsaki da kuma gwamnonin jam’iyyar aniyar shugabancin jam’iyyar na kasa wajen karbar madafun iko daga jam’iyyar APC.