A ranar Litinin gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya za su yanke shawara kan makomar Shugaban Jam’iyyar ta kasa, Prince Uche Secondus.
Shugaban Kungiyar Gwamnonin kuma Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ne zai jagoranci taron da za a gudanar a Abuja.
- Yajin Aiki: Gwamnati ta sa wa likitoci dokar ‘ba-aiki ba-albashi’
- ’Yan bindiga sun sace Kwamishina a Neja
A yayin taron, gwamnonin za su tattauna matsalolin cikin gida da ya kai ga wasu manyan jiga-jiganta bakwai ajiye mukamansu na shugabanci a jam’iyyar da kuma sake nazari kan bukatar Secondus ya yi murabus.
A bayan nan ne Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi da na Jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle da takwaransa na Kuros Riba Ben Ayade suka sauya sheka daga jam’iyyar zuwa APC mai mulki a kasar.
A halin yanzu dai Secondus na fuskantar matsin lamba kan ajiye mukaminsa kafin cikar wa’adinsa a watan Disambar 2021, lokacin da ake sa ran jam’iyyar za ta gudanar da taronta na kasa domin zaben sabbin shugabanni.
Aminiya ta rawaito cewa Secondus na fuskantar wannan matsi ne sakamakon sauya sheka da wasu manyan ’ya’yanta ke yi.
Kazalika, ana zargin Secondus da rashin tsarin shugabanci nagari ciki har da mayar da wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar saniyar ware wajen riko da akalar jagorancin jam’iyyar.
Majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa, taron gwamnonin zai bai Secondus damar tsare martabarsa wajen sauka daga mukaminsa cikin mutunci.
Bayanai sun ce gwamnonin za su tattauna kan dabaru tabbatar da nasarar jam’iyyar yayin zaben gwamnan Jihar Anambra da za a gudanar a 6 ga watan Nuwamba da kuma shirye-shiryen tunkarar babban zabe na 2023.