Gwamonin Jam’iyar APC mai mulkin Najeriya sun shiga taron gaggawa, kasa da mako guda kafin zaben shugaban kasa da ke tafe.
Shugaban APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, kira taron ne kan wasu batutuwa masu alakala da yakin neman zaben shugaban kasa da ’yan majalisar dokoki ta kasa da za a yi ranar Asabar.
- Ku ci gaba da karbar tsofaffin kudi – El-Rufa’i ga ma’aikatun gwamnatin Kaduna
- Yanzu matsalar canjin kudi ba za ta shafi zabe ba – Shugaban INEC
Tun kafin fara taron sirrin, wanda ke gudana a Sakatariyar Jam’iyyar APC ta Kasa, an tsaurara jami’an tsaro a yankin.
Ganawar sirrin na zuwa ne a daidai lokacin da wasu daga cikin gwamnonin APC suka bijire wa umarnin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na haramta amfani da tsoffin takardun Naira 1,000 da N500.
Idan ba a manta ba, gwamnonin jihohi 12, ciki har da na APC sun maka Gwamnatin Shugaba Buhari a Kotun Koli suna neman kotun ta soke umarnin gwamnatin na haramta amfani da tsoffin takardun Naira 1,000 da N500.
Karin bayani na tafe.