✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnoni sun maka Buhari a Kotu kan zargin karkatar da dukiyar kasa

Sun zargi Buhari da take hakkoki a daidai lokacin da yace yana yaki da cin hanci da rashawa.

Gwamnonin Jihohi 36 na Najeriya sun maka Shugaba Muhammadu Buhari a gaban kuliya kan zarginsa da karkatar da kudaden da aka kwato daga hannun barayin gwamnati.

Gwamnonin na zargin gwamnatin Shugaba Buhari da karkatar da kudin da ya kai naira triliyan guda da biliyan dubu 800 daga cikin kudaden da aka kwato daga hannun wadanda suka saci kudaden gwamnati.

Karar da aka shigar a Kotun Koli ta kuma kunshi karkata akalar kadarorin da kudin su ya kai naira biliyan 450  daga cikin wadanda aka kwato tun daga shekarar 2015.

Jihohin na zargin gwamnatin tarayya da kin biyan wadannan makudan kudade a asusun tarayya da kuma karkata akalar su zuwa wasu asusun ajiya na daban sabanin abinda dokar kasa ta tanada.

Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanadi cewar duk wasu kudaden shigar da kasar ke samu za a zuba su ne cikin asusu guda ta hanyar da za a rika raba su kamar yadda doka ta tanada.

Jihohin Najeriyar na zargin Gwamnatin Tarayya da yin choge wajen karkata wadannan kudaden domin amfanin kan ta, saboda haka suna bukatar Kotun Koli da ta bukace ta da ta dawo da kudaden asusun tarayya domin raba su kamar yadda doka ta tanada.

Jihohin sun kuma bukaci gudanar da bincike domin gano yawan kudaden da aka samu daga cikin wadanda ake kwatowa a hannun barayin gwamnati tun daga shekarar 2015 lokacin Shugaban Buhari ya karbi akalar jagorancin kasar.

Gwamnonin a karkashin jagorancin Gwamnan Ekiti da ke zaman Shugaban Kungiyar Gwamnoni ta NGF, Kayode Fayemi, sun dauki tawagar kwararrun lauyoyi wanda Femi Falana zai jagoranta domin wakilatar su a karar da suka shigar ranar Litinin.

Sashen Hausa na Gidan Rediyon Faransa RFI ya ruwaito cewa, Gwamnonin sun zargi shugaba Buhari da take hakkokin jihohin kasar a daidai lokacin da yace yana yaki da cin hanci da rashawa.

Dokar kasa ta bai wa Kotun Koli hurumin sauraron kara tsakanin gwamnatocin jihohi da kuma tarayya a kan batutuwan da suka shafi kundin tsarin mulki.