✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnoni 6 da za su san matsayinsu yau a Kotun Koli

Ga jerin jihohin — hudu daga Arewa da kuma biyu daga Kudu — da gwamnoninsu za su san ainihin matsayinsu da makomar kujerarsu:

A yau Kotun Koli ta Najeriya za ta yanke hukunci kan shari’ar zaben gwamnonin jihohi shida da ake kalubalayar nasararsu a zaben ranar 18 ga Maris, 2023.

Ga jerin jihohin — hudu daga Arewa da kuma biyu daga Kudu — da gwamnoninsu za su san ainihin matsayinsu da makomar kujerarsu:

  1. Kano
  2. Zamfara
  3. Filato
  4. Bauchi
  5. Legas
  6. Ebonyi

1- Kano: Abba da Gawuna

Shari’ar Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano da Nasiru Yusuf Gawuna ita ce mafi zafi, ta fuskoki da dama.

Ita ce shari’ar da tun da farko ta yamutsa hazo inda a ranar 20 ga Satumban 2023 kotun sauraron karrrakin zabe ta kwace kujerar Gwamna Abba, wanda ya lashe zaben, inda ta soke masa ƙuri’a 165,633, da cewa na bogi ne, wanda hakan ya sa ƙuri’a 1,019,602 raguwa,  Gawuna mai kuri’u 890,705 ya sha gabansa.

Abba wanda ya kayar da jam’iyya mai ci, da jam’iyyarsa, NNPP sun daukaka kara, amma hukuncin kotun daukaka karar ya bar baya da kura, saboda abubuwa masu karu da juna.

A zaman kotun, ta tabbatar da hukuncin kotun farko, amma ta bude wani sabon babi, cewa Abba ba dan halastaccen dan takara ba ne, saboda babu sunasa a rajistar mambobin NNPP.

Hakan ake ganin mayar da hannun agogo baya ne, kasancewar kotun farko ta bayyana cewa ba ta da hurumin sauraron lamarin saboda na kafin zabe ne, amma alkalan da aka daukaka kara gabansu suka ce tana da hurumi.

Amma takardar hukuncinta kuma ya nuna cewa dawo masa kujerarsa ta yi, daga bisani kuma take kokarin sauya rubutaccen hukuncin da ta ce akwai kurakurai a ciki.

2- Zamfara: Dauda Lawal da Matawalle

Shari’ar zaben gwamnan Zamfara na daga cikin mafiya zafi, musamman ganin yadda aka samu tufka da warwara a hukunce-hukuncen da kotun suka yanke a kai.

Gwamna Dauda Lawal Dare na jam’iyyar PDP, wanda shi ma ya kayar da gwamna mai ci, ya je kotun koli ne neman ta tabbatar da nasararsa, wadda kotun daukaka kara ta soke, inda ta ba da umarnin a yi sabon zabe a wasu kananan hukumomi uku.

Abokin hamayyansa, kuma tsohon Gwamna Bello Matawalle da ke neman wa’adin mulki na biyu ne dai ke kalubalantar sa, inda ko kotun daukaka ta sa a sake gudanar da zabe a wuraren da ba a yi zaben amma ba ko kuma ba a kirga sakamakonsu ba.

Mayawalle na APC, wanda yanzu shi ne karamin ministan tsaro, Dauda Lawal ya kayar da shi ne da kuri’a 377, 726, amma tsohon gwamnan na zargin hukumar zabe da jawo faduwarsa saboda gazawarta wajen  hada sakamakon wasu mazabu.

Kotun sauraron karar zaben gwamnan Zamfara dai ta kori karar da shigar gabanta a matsayin mara tushe, amma da da ya kotun daukaka kara kuma, sai ta ba shi nasara, hukuncin da Gwamna Dauda Lawal Dare ya daukaka kara a kai zuwa  kotun koli yana neman ta soke, ta tabbatar da nasararsa.

3- Filato: Mutfwang da Goshwe

Gwamna Caleb Mutfwang na PDP na Filato shi ma dan takarar APC mai mulki a jihar, Nentawe Goshwe ya kayar.

Shari’ar gwamnan Filato ta dauki hanali ne musamman saboda tufka da warwara a hukuncin kotunan farko kan batun halascin takarar Gwamna Mutfwang, lamarin da a kansa kotunan baya suka kwace kujerar ’yan jam’iyyarsa a majalisar dokoki ta kasa.

Gwamna Mutfwang ya je kotun koli ne bayan a watan Nuwamba kotun daukaka kara ta soke zabensa, ta kuma umarci hukumar zabe (INEC) ta bai wa abokin shari’arsa shaidar cin zaben.

Wannan ya saba da hukuncin hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben wadda ta tabbatar da nasararsa, wadda a cewarta ’yan jami’yar adawa ba su da hurum tsoma baki kan yadda wata jam’iyya ta zabi shugabanninta.

Hakan ta sa gwamnan zuwa kotun koli neman ta tabbatar da hukuncin kotun farko.

4- Bauchi: Bala Kaura da Sadique

A Bauchi kuwa dan jam’iyyar adawa ta APC, Saddique Abubakar ne ke kalubalantar Gwamna Gwamna Bala Mohammed na PDP, da ya yi tazarce, a gaban kotun koli.

Sadique ya je kotun koli ne duk da cewa kotun sauraron kararrakin zaben da ta daukaka kara sun kori kararsa da cewa ba shi da tushe.

Sadique na kalubalantar sakamakon zaben ne bisa hujjar saba dokar zabe da kuma rashin cike takardun zabe yadda ya kamata; zargin da kotun daukaka kara ta ce ya gaza gabatar da gamsassun hujjoji da shaidu da za su tabbatar.

Daga nan kuma ya tafi kotun koli yana mai kwarin gwiwar za ta sake duba hujjojin da ya gabatar ta ba shi kujerar, Bala kaura kuma na fatan kotun ta tabbatar da hukuncin kotunan baya.

5- Legas: Sanwo-Olu, GRV da Jandor

A Legas ma gwamnan da ya samu wa’adi na biyu, Babajide Sanwo-olu na APC ake kalubalanta, inda dan takarar LP, Gbadebo Rhodes-vivour da takwaransa na PDP, Abdulazeez Adeniran suka suke je kotu.

Kafin yanzu, kotunan farko sun yi watsi da shari’o’insu, saboda a cewarta ba su da tushe

Amma masu kara na kafa hujja da cewa Sanwo-Olu da mataimakinsa Obafemi Hamzat ba su cancanci tsayawa takara ba.

6- Ebonyi: Nwifuru da Odii

Dan takarar jam’iyyar APGA, Bernard Odoh wanda ya zo na uku a zaben ya maka Gwamna Nwifuru na APC a kotu domin neman a ba shi kujerar.

A ranar Litinin kotun ta kammala sauraron bahasin bangarorin da ke shari’ar wadda ɗan takarar jam’iyyar PDP kuma wanda ya zo na biyu a zaɓen gwamnan, Chukwuma Ifeanyi Odii ya daukaka.

A watan Nuwamba kotun daukaka kara ta kori karar Oddi da PDP da cewa ba su da hurumin yin katsalandan cikin harkar jam’iyyar APC wajen zaben dan takara.