Ministan Masana’antu da Sana’oi, Otunba Richard Adeniyi Adebayo, ya ce tsarin farko na farfado da tattalin arzikin da Gwamnatin Tarayya za ta gudanar zai samar da ayyuka tare da hana ayyuka miliyan biyar durkushewa.
Gwamnatin Tarayya ta bijiro da tsarin ne domin magance tabarbarewar tattalin arzikin kasa ne sakamakon annobar COVID-19.
Ministan ya ce akwai tsari a kasa da zai hana durkushewar akalla ayyukan ‘yan Najeriya miliyan daya da dubu dari hudu, wanda kashi 40 kananan sana’oin mata ne da nakasassu.
Adebayo ya bayyana hakan ne a cikin wata takarda da Mai Taimaka Masa a Harkokin Yada Labarai, Julius Toba-Jegede, ya sanya wa hannu ranar Alhamis.
- Za a fara daukar sabbin ‘yan N-Power —Minista
- Gaskiya ne ba mu biya ‘yan N-Power 12,000 hakkokinsu ba —Gwamnati
Ministan ya kara da cewar wannan wani yunkuri ne da ma’aikatarsa ke yi na ganin an yi nasara a shirin Gwamnatin Tarayya na farfado da tattalin arzikin a wannan yanayin da duniya take ciki na annoba.
Ya ce, domin samun nasara akan hakan, sun bijiro da shiri guda uku kamar haka:
- Asusun da zai tallafa wa masu matsakaita da kuma kananan sana’oi.
- Shirin da zai bayar da tallafai ga masu son fara sana’oi.
- Sai kuma tsarin bayar da rance ga matsakaita da kuma kananan sana’oi don su tsaya da kafafunsu.
Ya ce, shiri zai samar da ayyuka miliyan biyar, ya taimaka wa masana’antu wajen gudanarwa da kare su daga durkushewa da kuma habbaka sana’oin masana’antun, tare kuma da hana su jin radadin annobar ta COVID-19.