✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Gwamnatin ta ce ta kashe kuɗaɗen ne saboda wahalhalun da koma bayan tattalin arziƙi ya samu.

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana cewa magidanta 809,202 sun amfana da tallafin Naira biliyan 3.91 a 2024, domin rage wahalhalun da tattalin arziƙin ƙasa ke fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur.

Gwamna Buni, wanda mataimakinsa Idi Barde Gubana ya wakilta, ya bayyana hakan a Damaturu yayin taron ƙarshen shekara da manema labarai.

Ya ce sama da mutum 201,300 sun samu alawus-alawus don taimakon iyalansu saboda rikicin Boko Haram da aka kwashe shekaru ana yi.

Hakazalika, wasu magidanta 456,205 da mutum 975,220 sun samu tallafin abinci sakamakon ambaliyar ruwa da rikicin Boko Haram.

Gwamnan, ya ce gwamnatin Yobe ta kashe Naira biliyan 15.3 wajen sayen abinci da kayan noma don tallafa wa manoma 5,340 a ƙananan hukumomi 17 na jihar.

Bugu da ƙari, jihar ta samu kyautar dala 500,000 (kwatankwacin Naira miliyan 800) daga wani shirin kiwon lafiya a yankin Arewa maso Gabas.

Ya kuma tabbatar da cewa nakasassu ba a bar su a baya ba, inda aka raba musu kekunan guragu 350 a watan da ya gabata.

Shugaban ƙungiyar ’yan jarida ta ƙasa (NUJ), Rajab Ismail, ya yaba wa gwamnatin Buni kan samar da yanayin da ke bai wa ‘yan jarida damar aiki ba tare da tsoro ba.

Ya kuma tunatar da su muhimmancin bin ƙa’idar aikin jarida a lokacin zaɓe.