Gwamnatin jihar Yobe da asusun bayar da tallafi na Majalisar Dinkin Duniya UNDP, ta raba naira miliyan 75 don tallafa wa Mata 1,500 ‘yan gudun hijira da aka sake tsugunar da su a jihar.
Wakilin Aminiya ya ruwaito cewa an raba kudaden ne karkashin shirin nan na taimakawa gajiyayyu a matsayin tallafi don su fara sana’ar da za su dogara da kansu.
- PDP ta dakatar da Sanata Bello Hayatu Gwarzo
- Kungiyoyin Ingila sun janye aniyar shiga gasar Super League
Yayin taron bayar da tallafin, Gwamna Mai Mala Buni, ya ce a kwanan nan ne suka raba Awakai da naira dubu 10 ga wasu Mata biyar a dukkan mazabu 178 da ake da su a fadin jihar Yobe.
Aminiya ta ruwaito cewa, Mata dubu 3000 ne suka amfana da tallafin a karkashin Ma’aikatar kula da harkokin Mata, sannan aka basu naira dubu 20 kowacce don yin sana’ar kosai da cin-cin da awara
Gwamnan ya yabawa UNDP kan yadda suka hada karfi da karfe wajen sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar da kuma ba su tallafin dogaro da kai.
“Ina mai godiya ga asusun Majalisar Dinkin Duniya na UNDP bisa tallafin da suka bayar wajen sake Gina kasuwa da samar da ababen more rayuwa.
Muna kuma yaba musu kan raba iri na amfanin gona, da yin kwaskwarimar makarantun Firamare da samar da kayan aikin a babban asibiti na Buni Yadi”
A karshe, Mai Mala ya yi kira ga wadanda suka ci moriyar shirin da cewa suyi amfani da tallafin yadda dace wajen bunkasa sana’oinsu don tsare mutuncin su.
A jawabin sa, Babban Sakataren Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar SEMA, Dokta Muhammad Goje ya bayyana iin dadinsa ya yi wa gwamna Mai Mala Buni a madadin wadanda suka samu tallafin.
Ya ja hankalin Babban Daraktan Kananan bankuna, Dokta Sherrif Almuhajir, da tawagarsa da su tabbatar sun bi tsare-tsaren da aka shimfida don biyan dukkan Matan da za su ci gajiyar cikin sa’a 72 daga lokacin da aka kaddamar da fara biyan.
Kazalika, Dokta Goje ya bukaci hadin kansu wajen tabbatar da bin tsari yayin biyan kudaden da kuma ba da bahasin duk wata matsala da ta taso wacce ba’a shirya mata ba.