✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Yobe Ta Gina Kamfanin Sarrafa Ridi A Kan N3.6bn

A kokarinta na habaka noman ridi da taimaka wa manoma, gwamnatin Yobe ta samar da kamfanin sarrafa ridi da babu na irinsa a Najeriya a…

A kokarinta na habaka noman ridi da taimaka wa manoma, gwamnatin Yobe ta samar da kamfanin sarrafa ridi da babu na irinsa a Najeriya a kan kudi Naira biliyan 3.6.

Bayanin hakan  dai ya fito ne daga Kwamishinan Kasuwanci, Masana’antu da Yawon Bude Ido na jihar, Kaigama Umar Yayin, a lokacin da ya ke jawabi ga manema labarai a garin Machina.

Kaigama Umar ya kara da cewar, bayan wannan kamfanin sarrafa ridi dake garin Machina wanda tunin aka kammala shi, akwai sauran irinsa guda uku da ake kokarin kammala gina su a garuruwan Potiskum, Nguru, da Damaturu nan ba da jimawa ba.

Ya kara bayyana cewa, “tunanin kafa masana’antar tsaftace ridi da sarrafa shi Gwamna Mai Mala Buni ne ya kirkiro shi jim kadan bayan hawansa mulki da nufin kara karfin gwiwa ga manoman ridi don sake habaka wannan noma nasu.”

Ya Kara da cewar, ya hakkake cewar, irin wannan kokari na gwamnati zai kara taimaka wa manoman don ci gaba da kokarinsu a bangaren, wanda kan iya sake habaka tattalim arzikinsu da na jihar Yobe baki daya.

A cewarsa, a saninsa Jihar Yobe ita ce kan gaba wajen noman ridi  a kasar, inda inda ake noman ridin don kasuwanci musamman a yankunan Geidam, Yunusari, Nguru da Machina da dai sauransu a jihar.

Alhaji Kaigama ya kara tabbatar da cewar, kafa masana’antar ridin zai taimakawa manoman matuka kasancewar a baya sai sun dauki ridinsu zuwa garin Kano don sarrafa shi amma a yanzu nesa ta zo kusa.

Daga nan ya kirayi Masu zuba hannun jari daga kowane yanki na kasar nan da ma kasashen ketare da su zo jihar musamman ta zuwa don sayen ridin da za a fara sarrafawa don fita da shi ya zuwa kasashen ketare kasancewar jihar na da filin jirgin saman kasa da kasa mai daukar manyan jiragen dakon kaya da ke Damaturu.