✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tinubu ce za gudanar ad kidaya —Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a dage lokacin gudanar da Kidayar Jama'a da Gidaje da aka shirya farawa ranar 3 ga watan Mayu mai kamawa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a dage lokacin gudanar da Kidayar Jama’a da Gidaje da aka shirya farawa ranar 3 ga watan Mayu mai kamawa.

Kwana hudu kafin fara aikin Buhari ya ce ya bai wa gwamnati mai jiran gado damar yanke shawara kan lokacin gudanar da kidayar domin tabbatar da nasararsa.

Ya sake dage lokacin gudanar da kidayar ne bayan wata ganawa da tsakanin Shugaba Buhari da shugaban hukumar, Nasir Isa Kwarra tare da Majalisar Zartarwa ta Tarayya a ranar Juma’a a Fadar Shugaban Kasa.

Sanarwar da Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed ya fitar ta ce duk da haka Shugaba Buhari ya jaddada muhimmancin gudanar da kidayar wadda rabon da a gudanar shekara 17 ke nan.

Shugaban ya kuma yaba da kyakkyawatan shirin da hukumar ta yi wa kidayar, wanda zai tabbatar da ingancinsa kamar na sauran kasashen duniya.

Wata majiya a hukumar ta ce an dage aikin kidayar ne saboda wasu matsalolin da hukumar ke fuskanta da za su hana ta gudanar da aikin a lokaci guda; sai dai ba ta yi karin bayani ba.

Idan za a tuna, Hukumar Kidaya ta Kasa ta dage aikin daga 27 ga watan Maris zuwa ranar 3 ga watan Mayu, saboda kauce wa cin karo da zaben gwamnoni da aka kara wa lokaci.

A baya-bayan nan hukumar ta dakatar da horar da ma’aikatan wucin-gadi da za su gudanar da aikin, saboda matsalolin kudi da na jigila da sauransu.

A ranar Alhamis shugaban hukumar kidayar, Nasir Isa Kwarra ya shaida wa wakilan kasashen waje a Abuja cewa ba duka na’urorin aikin da hukumar take bukata ne suka shiga hannunta ba.

Amma ya ce nan gaba kadan hukumar za ta karbi cikon na’urori 300,000 da suka rage daga cikin na’urori 800,000 da za a yi amfani da su.

Duk bayan duk shekara 10 ake gudanar da kidaya Najeriya, amma yanzu shekara 17 tun tun bayan wanda kasar ta gudanar a shekarar 2006.

 

Daga: Sagir Kano Saleh da Faruk Shuaibu da Muideen Olaniyi.