✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Tarayya za ta kashe N30bn don gyaran majalisa 

Gwamnatin Tarayya ta ce gyaran Majalisar Dokoki ta Kasa zai lakume Naira biliyan 30.2

Gwamnatin Tarayya ta ce aikin gyaran Majalisar Dokoki ta Kasa  zai lakume Naira biliyan 30.2.

Ministan Babban Birnin Tarayya, Musa Mohammed Bello, ne ya bayyana hakan a yayin wani rangadin wasu ayyuka da Kwamitin Majalisar Dattijai ya gudanar a ranar Alhamis.

An ware Naira biliyan 37 domin gudanar da aikin gyaran a kasafin kudin 2020 amma aka rage shi zuwa Naira biliyan 9.25 lokacin da aka sake duba kasafin a tsakiyar shekara.

Sai dai Ministan ya shaida wa kwamitin majalisar cewa kudin kwangilar aikin ya kai Naira biliyan 30.2 wanda aka biya Naira biliyan 9.2 ga ’yan kwangilar.

Ya ce kwangilar wadda ta fara a ranar 16 ga Afrilu, 2022, za a kammala ta ne a ranar 15 ga Agusta, 2023.

Ya bayyana cewa ba a taba yi wa Sashena II na Majalisar Dokokin wani aikin gyara ba tun da aka gina shi a 1999.

Ministan ya zayyana wasu muhimman ayyuka da Gwamnatin Tarayya ta fara da su hada da gyara ginin Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da kuma gina hanyar shiga majalisa da bangare kudu.

Sauran, ya ce sun hada da gyara aikin fadada titin Kudancin hanyar Outer, samar da kayayyakin aikin injiniyoyi ga gundumar Wuye, gyarawa da fadada titin Shataletalen Villa na Kudancin hanyar Outer da kuma kammala titin B6, B12.

Sai dai ya ce karancin kudi ya sa ba a ba da fifiko ga wasu ayyukan ba don kammala su a kan lokaci.

Ministan ya ce: “Abin da muka yi shi ne saboda karancin kudi, mun ba da fifiko ga muhimman ayyukan more rayuwa domin kammala su.

“Kuma wajen yanke shawarar wadanda suka fi dacewa, mun duba wadanda suka fi muhimmanci ga mutane.

“Dukkan ayyukan guda hudu da muka ziyarta, mun gano cewa, duk ayyukan tituna ne da ake son hada wani sashe na birnin Abuja.

“An yi tsarin ta yadda za su dace da juna.

“Don haka, idan an gama kashin farko ba a gama dayan ba, to ba za a samu cikakkiyar fa’idar hanyar ba.”

Shugaban Kwamitin Majalisar Dattijai kan Babban Birnin Tarayya, Sanata Tolu Odebiyi, wanda ya jagoranci mambobin kwamitin, ya bayar da tabbacin cewa za a bai wa muhimman ayyuka fifiko ta fuskar kasafin kudi.

Ya ce, “Mun yi imanin cewa a wata mai zuwa, yana da muhimmanci mu kayyade duk ayyukan da ake yi, tare da fifita wadanda ya kamata a kammala kafin karshen wannan wa’adin.

“Za mu tabbatar mun samar da isassun kudade a kasafin kudi.

“Nan ba da dadewa ba za a mika mana kasafin kudinsu kuma yana da muhimmanci mu zo mu ga yanayin aikin da yadda shirin ya kammala kafin a kammala su.

“Kamar kowane aiki, za mu tabbatar da cewa duk ayyukan da ake bukatar su a kan lokaci an ba su fifiko.”