✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Tarayya za ta gana da El-Rufai da NLC

Ministan Kwadago zai yi zama da bangarorin a ranar Alhamis.

Gwamnatin Tarayya za ta yi zama da Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) da kuma Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai kan dambarwar da bangarorin ke yi kan sallamar ma’aikatan Jihar.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Kwadago ta Tarayya, Charles Akpan, ya ce za a yi zaman ne da misalin karfe 11 na safiyar Alhamis a Abuja.

“Mininstan Kwadago da Ayyuka, Dokta Chris Ngige zai jagoranci zaman sulhu tsakanin Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da Kungiyar Kwadago ta Najeriya,” inji takardar gayyatar da ya aike wa a ranar Laraba.

Akpan ya ce Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa, Ayuba Wabba zai jagoranci bangaren ’yan kwadago a yayin zaman.

Hakan na zuwa ne bayan sa-toka-sa-katsi tsakanin ’yan kwadago da ke yajin aikin gargadi na kwana biyar da kuma zanga-zangar lumana saboda sallamar dubban ma’aikatan da El-Rufai ya ce babu gudu, babu ja da baya a kai.

A ranar Laraba, El-Rufai ya yi barazanar dandana wa Shugaban NLC, Ayuba Wabba da sauran shugabannin ’yan kwadago kudarsu, ta yadda ba za su kara marmarin zuwa Jihar Kaduna ba.

Gwamnan wanda tun da farko ya ayyana su a matsayin wadanda ake nema ruwa a jallo, na zargin su da gurgunta tattalin arzikin jiharsa da lalata kayan gwamnati.

A ranar Larabar ya sanar da korar daukacin ma’aikatan jinya da ke kasa da mataki na 14 saboda sun shiga yajin aikin da NLC ta kira, ya kuma ba da umarnin a dauki sabbi da za su maye gurbinsu.

Ya kuma yi barazanar korar ma’aikatan Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) da ba su je wurin aiki ba a lokacin yajin aikin a yayin da Kungiyarsu ta ASUU ta umarce su da su yi watsi da barazanar tasa.

A halin yanzu dai kusan daukacin kungiyoyin ma’aikata a Jihar sun shiga yajin aikin da NLC ta kira, wanda ke neman rikidewa ya koma na gama-gari a fadin Najeriya.