Gwamnatin Tarayya, ta ƙaddamar da aikin gina rukunin gidaje masu ɗaki ɗaya da biyu da uku ƙarƙashin shirin renewed hope guda 250 a Jihar Gombe.
A lokacin dasa tubalin ginin gwamnan jihar, Inuwa Yahaya da ministan gidaje da raya birane, Ahmed Musa Dangiwa da ƙaramin minista Abdullahi T. Gwarzo, ne suka ƙaddamar da ginim rukunin gidajen a kan hanyar Gombe zuwa Bauchi.
- Ya kamata Tinubu ya bayyana kadarorinsa bayan shekara ɗaya a kan mulki — SERAP
- APC ta shiga ruɗani a Zamfara
Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ƙaddamar da tubalin ginin, gwamnan jihar, ya bayyana jin daɗinsa kan zaɓen Gombe a matsayin ɗaya daga cikin jihohin da shirin zai yi gwaji a shiyyar Arewa maso Gabas.
Ya bayar da tabbacin gwamnatinsa na ci gaba da goyon bayan g manufofin Shugaba Tinubu.
Da yake jawabi, ministan gidaje da raya birane, Dangiwa ya bayyana cewa gidajen a matsayin wani shiri na gwamnatin tarayya da ke da nufin magance matsalar ƙarancin gidaje a Najeriya da kuma samar da gidaje masu sauƙi ga ‘yan ƙasa.
Ya ce kashin farko na aikin gwamnati na da niyyar samar da gidaje 50,000 a faɗin Najeriya, inda za a fara da jihohi biyu daga kowace shiyya, inda aka zabi jihohin Gombe da Yobe daga yankin Arewa Maso Gabas.