Tun bayan da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCON), ta buƙaci kowane maniyyaci ya kara kusan Naira miliyan Biyu, ake ta tsotsan tsamiya a ƙasar nan.
Dalilin da tuni wasu maniyyatan suka fara neman a dawo musu da kuɗinsu, tunda a cewar wasu, ba su da kuɗin da za su cika a tsukukun kankanin lokaci.
- Kisan Sojoji: Basaraken da ake nema ya miƙa kansa ga ’yan sanda
- Hajji: Gwamnonin Kogi, Kebbi da Kano sun tallafa wa maniyyata
Aminiya ta ruwaito cewa, NAHCON ta sanya wa’adin ranar 28 ga watan Maris a matsayin ranar ƙarshe ga masu halin ciko wadannan kudade za su ciki.
Sai dai tun kafin wannan rana, gwamnonin wasu jihohi suka bayyana cewa za su tallafa wa maniyyatan da wani kaso na kuɗin da aka ƙara musu.
Jihar Kogi, Kano, Kebbi, Ogun da Sakkwato na da ga cikin jihohin da gwamnoninsu suka sha alwashin taimaka wa maniyyatan domin cika burinsu na sauke farali.
Haka kuma, wani bincike ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 900 domin tallafa wa maniyyatan Najeriya, dalili ke nan da ƙarin da maniyyatan za su yi bai haura wanda aka NAHCON ɗin ta sanar ba.
Wata majiya da ta buƙaci a sakaya sunanta ta ce, ba don tallafin gwamnatin tarayya ba, da kowane maniyyaci sai ya cika miliyan 3.5.
A yanzu dai an buƙaci kowane maniyyaci ya cika Naira miliyan 1.9 ne, sakamakon hauhawar farashin Dala da kuma karyewar darajar Naira.
Wata majiya mai tushe daga NAHCON, ta ce da tallafin da gwamnatin Najeriya ta bayar ya kai Naira biliyan 230, da ba za a buƙaci karin ko sisi daga wajen maniyyatan ba.
Gwamnatin ta bayyana cewar ta bayar da tallafi ne tun a ranar 28 ga watan Fabrairu 2024, yayin kaddamar da shirye-shiryen aikin Hajjin bana a Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima.
Majiyar ta ce, NAHCON ta tuntubi gwamnatocin jihohin Najeriya kafin gabatar da wannan ƙarin da karyewar darajar Naira ya janyo.
“A lissafin da aka yi a baya, Naira biliyan 90 da Gwamnatin Tarayya ta bayar, za ta iya cika wa maniyyata 19,000 tallafin Naira miliyan 3.5 ne kaɗai.
“Amma tun da maniyyatan 50,000 ne, gwamnatin tarayya ta iya bai wa kowane maniyyaci tallafin Naira miliyan 1.6 kaɗai.
“Dalilin da ya sa aka ce kowane maniyyaci ya ciko Naira miliyan 1.9 kenan,” in ji majiyar.
Wata majiya a fadar shugaban kasa, ta ce ba abin mamaki ba ne don gwamnatin tarayya ta bayar da wannan tallafin.
Da aka tuntubi kakakin NAHCON, Fatima Sanda Usara kan batun ta ce, “Abu ne mai wahala a iya kididdige iya abin da Gwamnatin Tarayya ta yi wa NAHCON, idan mun kammala, za mu sanar da kowa abin da aka yi.”