Gwamnatin Tarayya a Najeriya ta bayyana ranar Juma’a, 25 da kuma ranar Litinin, 28 ga watan Dasumban 2020 a matsayin ranakun hutun bukukuwan Kirsimeti.
Gwamnatin ta kuma bayyana ranar Juma’a 1 ga watan Janairun 2021, a matsayin ranar hutun sabuwar shekara.
- Buhari ya gana da Jonathan kan rikicin siyasar kasar Gambiya
- Buhari ya yi ta’aziyyar rasuwar Muhammad Lele Mukhtar
Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya.
Wata sanarwa da babban sakataren Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Dokta Shuaib Belgore ya sanya wa hannu a madadin Ministan, ta ce, “Dole ne mu yi koyi da rayuwar tawali’u, hidimtawa al’umma, jin kai, hakuri, zaman lafiya da kuma adalci a yayin da muke murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Isa.
A yayin da ya ke taya al’ummar Kiristan Najeriya da na sauran kasashen duniya murnar bikin Kirsimeti da Sabuwar Shekara, Aregbesola ya bukaci Kiristocin da su yi koyi da dukkanin wata koyarwa ta Annabi Isa da wadanda suka biyo tafarkinsa.
Kazalika sanarwar da Ministan ya fitar ta janyo hankalin ’yan Najeriya a kan su yi taka-tsan-tsan da matakan kariya wanda mahukuntan lafiya suka shar’anta domin dakile yaduwar cutar Coronavirus.