✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya ta musanta nuna kabilanci wajen kwaso ’yan Najeriya daga Sudan

Masar ta bayar da izinin a kwaso ’yan Najeriya ta cikinta bayan Buhari ya nemi alfarma.

Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da zarginta da nuna bangaranci ko kuma kabilanci wurin kwaso ‘yan Najeriyar da ke Sudan.

A wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an ga wani mutum yana magana da harshen Igbo inda ya bayyana cewa an ki kwaso wasu daga cikinsu saboda kabilanci.

Sai dai a wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta fitar, ta bayyana cewa babu kamshin gaskiya a ikirarin da mutum ya yi.

“Ma’aikatar ta yi bincike kan zarge-zargen da ya yi kuma tana tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa babu gaskiya a zarge-zargen da ya yi.

“Ofishin Jakadancin Najeriya a Khartoum ya tabbatar da cewa ‘yan kabilar Igbo na daga cikin rukunin farko na ‘yan kasar 637 da aka kai iyakar Aswa a Masar inda suke jira a mayar da su Najeriya,” kamar yadda sanarwar Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriyar ta bayyana.

Hasali ma ma’aikatar ta wallafa hotunan wasu daga cikin ’yan kabilar Igbo da ke zaune a Sudan da ta kwaso.

Ma’aikatar ta kara da cewa kafin a soma kwasar ‘yan kasar zuwa kan iyaka, sai da aka samu rashin jituwa tsakanin daliban Najeriya da kuma ‘yan Najeriyar da ke zama a Sudan sakamakon karancin motoci.

Amma ma’aikatar ta ce duk da haka an samar da motoci domin kwasar duk wani dan Najeriya da ke zaune a Sudan kuma yake so ya bar kasar.

’Yan Najeriya da dama ne gwamnatin kasar ta kwaso daga Sudan sakamakon rikicin da ake yi a kasar, sai dai an samu tsaiko wurin mayar da su Najeriyar sakamakon wasu dalilai.

Daga ciki kuwa har da jinkirin da aka samu wurin kwaso su da kuma makalewar da ’yan kasar suka yi kan iyakar Masar da Sudan sakamakon kin bude iyakar da Masar din ba ta yi ba ga ’yan Najeriya.

An kwaso ’yan Najeriya daga Masar

Rahotanni sun bayyana cewa an kwaso rukunin farko na ’yan Najeriya da suke kokarin tserewa rikicin da ya barke a Sudan.

Bayanai sun ce an kwaso ’yan Najeriyar ne daga filin jirgin saman Aswan da ke kasar Masar.

Tun da farko dai an sa ran tasowar ’yan Najeriyar da misalin karfe 1 na rana a jirgin Sojin Saman Kasar na NAF C130 da wani jirgin Air Peace da fasinjoji 274, amma hakan bai samu ba.

Lamarin na zuwa ne bayan da hukumomin Masar suka shardanta cewa dole ne duk wadanda za a kwashe su bar kasarsu nan take.

Majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa, an ba wa mutanen damar shiga filin jirgin saman Masar ne tsakanin daren jiya zuwa safiyar Laraba.

Buhari ya nemi alfarmar takwaransa na Masar

A bayan nan ne dai Gwamnatin Masar ta ce ta yarda a kwashe ’yan Najeriya da ke tsere wa fadan da ake yi a Sudan ta kasarta.

Shugabar Hukumar Kula da ’Yan Najeriya Mazauna Ketare NiDCOM, Abike Dabiri-Erewa ce ta tabbatar da wannan lamari a ranar Litinin.

A cewarta, Gwamnatin Masar ta bayar da lamunin ne bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi alfarma daga wajen takwaransa na Masar din, Shugaba Abdel Fattah El-Sisi.