✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin tarayya ta lashe amanta game da kudin Abacha

Gwamnatin tarayya ta ce ta yi kuskure a bayanin da ta yi a baya na yadda za ta kashe kudaden da aka dawo mata da…

Gwamnatin tarayya ta ce ta yi kuskure a bayanin da ta yi a baya na yadda za ta kashe kudaden da aka dawo mata da su a baya-bayan nan daga cikin dukiyar da marigayi Janar Sani Abacha ya ajiye a kasashen waje.

Gwamnatin ta ce za ta yi amfani da kudaden ne wajen aiwatar da wasu ayyuka guda uku daga cikin muhimman ayyuka biyar da ta sa a gaba, sabanin yadda ta bayyana tun farko.

Ayyukan, a cewar gwamnatin, ba su kunshi aikin samar da wutar lantarki na Mambila da aikin hanyar da ta hada shiyyoyin Kudu Maso Gabas da Kudu Maso Yammacin Najeriya ba.

Babban mai taimaka wa shugaban kasa a kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, shi ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a shafinsa na Twitter.

Kudaden, wadanda yawansu ya kai dala miliyan 311, an dawo da su ne daga kasashen Amurka da yankin Jersy bayan da Najeriya ta kamala cika sharuddan da aka gindaya mata.

A cewar sanarwar, ko da yake tun da farko Asusun Fadar Shugaban Kasa kan Ayyukan Raya Kasa ya amince a yi amfani da kudaden wajen dukkan ayyukan guda biyar, gwamnatin za ta fi mayar da hankali ne kawai a kan ayyuka guda uku, kamar yadda yarjejeniyar dawo da kudaden ta tanada.

A ina kudin suke?

Malam Garba Shehu ya ce ayyukan sun hada da ginin Gadar Kogin Neja ta Biyu, da aikin titin da ya tashi daga Abuja ya bi ta Kaduna zuwa Kano, sai kuma aikin titin da ya tashi daga Legas zuwa Badun.

Sanarwar ta kara da cewa kudaden na ajiye ne a asusun ajiyar Hukumar Zuba Jari ta Kasa wato NSIA.

A kwanan baya ne dai Malam Garba Shehu ya ambato aikin samar da wutar lantarki na Mabilla da hanyar da ta hade gabashi da yammacin Najeriya a cikin jerin ayyukan da za a yi da kudin.

Sai dai bai yi bayani dalla-dalla ba a kan nawa aka kashe zuwa yanzu a kan wadannan ayyukan da kuma abin da za a kashe don kammala su.