Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq, ta bayyana cewa gwamnati ta kaddamar da wani sabon shiri mai suna ‘N-Knowledge’ domin tallafa wa matasan Najeriya su koyi aikin yi a bangaren fasahar zamani.
Ministar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren ma’aikatar, Alhaji Bashir Nura Alkali ya raba wa manema labarai a makon jiya.
- Matsalar Tsaro: Sabuwar barazana ta kunno kai a Najeriya — Magashi
- Wasu matasa sun guntule wa juna hannu a Yobe
Alkali ya bayyana cewa an fara shirin ne a dukkan sassa shida na kasar nan tare da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
A cewarsa, “‘N-Knowledge’ wani bangare ne na shirin ‘N-Power’ wanda zai mai da hankali ga bai wa matasan Najeriya horaswar da ta kamata domin su zama kwararrun ma’aikata, masu kirkira kuma ‘yan kasuwa da za su iya yin aiki a nan gida da ketare.
“Shirin na ‘N-Power wato N-Knowledge zai horas da matasa 20,000 daidai da muradin duniya a matsayin wadanda za su iya aiki a kasashen ketare a bangaren fasahar sadarwar zamani.”
Babban Sakataren ya ce an tsara bangaren horaswa na shirin ne don bunkasa kwarewar matasan wajen kirkirar manhaja da horaswa kan hadawa da gyara kayan aikin komfuta wanda zai sanya Najeriya ta shiga sahun kasashen da ke tura ma’aikata zuwa wasu kasashen domin su yi aikin hada manhaja.
“Shirin ya kunshi tanadar matasa a wani kebabben wuri ana horas da su har tsawon wata uku sannan a ba su aikin wucin gadi na wata shida a dukkan sassa shida na kasar nan.
“Za a fara da jimillar mutum 20,000 da za su ci moriyar shirin.”
Ya kara da cewa a karshen shirin, matasan da aka gamsu da cancantar su daga horaswar da aka yi masu za a ba su satifiket da takardun shaida.
Ya ce, “A lokacin wannan tirenin din za a yi masu karatu daban-daban wanda ba shakka zai kara masu sanin makamar aiki har su kasance sun shirya wa shiga duk wata gogayya a duniya wajen aiki.
“Wannan yana da muhimmanci domin kuwa wadanda aka horas din za a koya masu darussan da za su amfane su a iya tsawon rayuwar su tare da sauya masu tunani, da dabi’u nagari na gudanar da aiki a yayin da kuma ake karantar da su ka’idojin yin mu’amala da juna.”