Gwamnatin Tarayya ta sanar da bankado wasu masu samar da kudi guda 96 don daukar nauyin ta’addanci da kuma masu alaka da kamfanonin hada-hadar kudi 424 da ke ba da gudunmuwar ta’addanci a kasar.
Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a yau Alhamis, yayin wani bayani da ya yi kan yaki da cin hanci da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi.
A cewarsa, Hukumar da ke Tattara Bayanan Sirri kan Kudade a Najeriya (NFIU) ta gano masana’antu 123 da kamfanonin 33 na masu musayar kudi da ke da alaka da ’yan ta’adda a Najeriya.
Ya ce, “A bangarenta, a sharhin da ta yi kan kudade na 2020-2021, ta bayyana masu hada-hadar kudade 96 da ke da alaka da ’yan ta’adda a Najeriya.
“Akwai kuma wasu 424 da ke samar da kudade domin ta’addanci da suka hadar da kamfanoni 123, da kuma na masu musayar kudi 33.
“Bugu da kari an gano wasu 26 da ake zargi da ta’addanci da wasu bakwai kuma da ake hada kai da su kan harkokin ta’addanci, inda wannan bayani ya kai ga kama 45 da ake zargi wadanda kwanan nan za a gabatar da su a gaban kotu,” a cewar Ministan.