Ma’aikatar Ilimi ta kasa ta tabbatar da ranar Litinin, 18 ga watan Janairun 2021 a matsayin ranar komawa makarantu a fadin Najeriya.
Tabbacin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ranar Alhamis mai dauke da sa hannun jami’inta yada labaran, Mista Ben Goong.
- Masarautar Zazzau: Lauyan Iyan Zazzau ya janye kara
- Jahilai ne ke juya al’amuran siyasa da gwamnati a Kano — Hadimin Ganduje
- An yi wa Sarki Abdullah II na Jordan rigakafin COVID-19
Sanarwar ta ce, “Bayan tuntubar masu ruwa da tsaki a matakai daban-daban da suka hada da kwamishinonin ilimi na jihohi da masu makarantu masu zaman kansu da shugabannin manyan makarantun gaba da Sikandire da Shugabannin kungiyoyin dalibai dana ma’aikata, sun bayyana ra’ayoyinsu kan a koma makaranta ranar 18, ga watan Janairun 2021 .
“Wajibi ne Iyaye da hukumomin makarantu su tabbatar da kiyaye matakan dakile yaduwar cutar COVID-19 da suka hada da sanya takunkumin rufe fuska a kan ilahirin dalibai da malamai da dukkan ma’aikatan makarantun.
Sanarwar ta kara da cewa, “Wajibi ne makarantun su tabbatar da samar da wadataccen ruwa da sunadarin tsaftace hannu da tabbatar da bayar da tazara da nesa-nesa da juna da kauracewa cunkoson jama’a da taron dalibai da rage yawan adadin masu kai ziyara.