Gwamnatin Tarayya ta amince da ƙarin kashi 50 na kuɗin abincin fursunonin da ke gidajen gyaran hali a faɗin Nijeriya.
Kakakin Hukumar Gidajen Gyara Hali na Nijeriya, Umar Abubakar ne ya bayyana hakan yayin yi wa manema labarai jawabi a Abuja.
- Ambaliya ta kashe mutane 20 da gidaje a Yobe
- Sabon albashi: Majalisar Kano ta amince da ƙarin kasafin N99bn
Ƙarin kuɗin ciyar da fursunonin ya biyo bayan wani faifan bidiyo na baya-bayan nan, inda fursunonin a wani gidan gyaran hali da ke Calabar a Jihar Kuros Riba suka koka da rashin wadataccen abinci.
Sai dai da yake yi wa manema labarai jawabin a ranar Alhamis, Umar Abubakar ya ce an ƙara kuɗin abincin ne la’akari da yanayin tsadar abinci da ake fuskanta a ƙasar.
Ya ce ƙarin zai fara aiki ne daga watan Agusta a wani yunƙuri na inganta rayuwar mazauna gidajen yarin.
“Kwana huɗu da suka gabata na yi tattaunawa a game da wani bidiyo da ake yaɗawa da ake zargin na abincin ’yan gidan yari ne.
“Tuni Hukumar Gidajen Gyara Hali ta kafa kwamitin bincike a kan bidiyon, sai dai ba zan yi magana sosai a kan sakamakon binciken ba.
“Amma saboda tsadar abinci, Gwamnatin Tarayya ta amince da ƙara kuɗin abincin furunoni da kashi 50, kuma wannan karo na farko na ƙarin ne.”
Ya kuma bayyana cewa mazauna gidajen yarin da dama suna karatu a jami’o’in Nijeriya, a cewarsa har da mutum shida masu karatun digirin digirgir (PhD), da kuma mutum 1,000 masu karatun digiri na farko a lokacin da suke zaune a gidajen yarin.
Hukumar Kula da Gidajen Yari wadda a halin yanzu akwai aƙalla fursunoni 84,575 da ke ƙarƙashin kulawarta, an ware sama da Naira biliyan 24.4 domin samar wa fursunoni kayayyakin abinci da sauran kayan buƙata a Kasafin Kudin 2024.
Bayanai sun ce an ɗauki matakin ne domin magance matsalolin da aka bayyana damuwa a kai a watan Disamba 2023, lokacin da aka bayyana cewa N750 ne kawai ake kashe wa kowane fursuna duk rana a matsayin kuɗin abinci, alhali ana kashe wa kowane kare ɗaya N800 duk rana domin hidimta wa karnuka 900 na hukumar.