✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Ginin Gidaje 250 A Gombe

Shirin na gwamnatin tarayya na da nufin magance matsalar ƙarancin gidaje a Najeriya.

Gwamnatin Tarayya, ta ƙaddamar da aikin gina rukunin gidaje masu ɗaki ɗaya da biyu da uku ƙarƙashin shirin renewed hope guda 250 a Jihar Gombe.

A lokacin dasa tubalin ginin gwamnan jihar, Inuwa Yahaya da ministan gidaje da raya birane, Ahmed Musa Dangiwa da ƙaramin minista Abdullahi T. Gwarzo, ne suka ƙaddamar da ginim rukunin gidajen a kan hanyar Gombe zuwa Bauchi.

Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ƙaddamar da tubalin ginin, gwamnan jihar, ya bayyana jin daɗinsa kan zaɓen Gombe a matsayin ɗaya daga cikin jihohin da shirin zai yi gwaji a shiyyar Arewa maso Gabas.

Ya bayar da tabbacin gwamnatinsa na ci gaba da goyon bayan g manufofin Shugaba Tinubu.

Da yake jawabi, ministan gidaje da raya birane, Dangiwa ya bayyana cewa gidajen a matsayin wani shiri na gwamnatin tarayya da ke da nufin magance matsalar ƙarancin gidaje a Najeriya da kuma samar da gidaje masu sauƙi ga ‘yan ƙasa.

Ya ce kashin farko na aikin gwamnati na da niyyar samar da gidaje 50,000 a faɗin Najeriya, inda za a fara da jihohi biyu daga kowace shiyya, inda aka zabi jihohin Gombe da Yobe daga yankin Arewa Maso Gabas.