✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin tarayya ce ya dace ta jagoranci afuwar barayin shanu

Afuwar farko da `yan kasar nan suka fara sani gwamnatin tarayya ta fara yi ga mutanen da suka dauki makamai a kan sauran al`ummar kasa,…

Afuwar farko da `yan kasar nan suka fara sani gwamnatin tarayya ta fara yi ga mutanen da suka dauki makamai a kan sauran al`ummar kasa, ita ce ta bayan kammala yakin basasasar kasar nan da kasar ta samu kanta tsakanin shekarun 1967zuwa 1970, bayan da gwamnan mulkin soja na Jihar Gabas a lokacin Laftanar Kanar Odumegwu Ojukwu ya yi ikirarin balle jihar daga tarayyar kasar nan. Bayan kammala yakin, da aka dauki watanni 30, ana yi, ya kuma yi sanadiyyar rasuwar sama da mutane sama da dubu 500, inda Gwamnatin Shugaba Janar Gowon ta yi afuwa musamman ga askarawan kasar nan da ma`aikatan gwamnati da suka shiga yakin a bangaren Biafara, amma ban da madugun tawayen Kanar Ojukwu, wanda shi sai a cikin shekarar 1983, gwamnati tarayya ta farar hula ta Shugaba Alhaji Shehu Shagari ta bayar da afuwa gare shi.
Shi ma Marigayi Shugaba Umaru Musa `Yar`aduwa a ranar 06-08-2009, ya yi tayin yin afuwa ga tsagerun yankin Neja Delta yankin da ya kunshi shiyyar Kudu maso Kudu mai arzikin man fetur, tsagerun da suka yi kaurin suna wajen fasa bututun man fetur da satar man da dai sauran ayyukan ta`addanci na yin garkuwa da mutane a yankin da sunan neman kudin fansa. Ta`addancin da bayan rashin zaman lafiya da ya rinka haddasawa, ya kuma rinka kawo koma bayan danyen man fetur da ake hakowa a yankin da kashi daya bisa uku (1/3). Afuwar ta kunshi bayar da kudi da horarwa a ciki da wajen kasar nan ga matasan da suka yarda suka mika makamansu.
Shirin yin afuwar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam`iyyar APC, a cikin jawabinsa na karbar mulki a ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata daga hannun gwamnatin PDP, da ta bullo da shirin afuwar, ya sha alwashin cewa gwamnatinsa, za ta ci gaba  da shi,tare da inganta shi.
Shirin yin Afuwa na uku da gwamnatin tarayya har gobe take ta begen ganin ta samu makamar yadda za ta yi shi, shi ne na `yan kungiyar Ahlis Sunnah Lid-Da`awati Wal jihad da ake yi wa lakabi da Boko Haram, `yan kungiyar da suke ta gwagwarmayar ganin sun kwace mulkin kasar nan tun a shekarar 2009, wadda kuma ta yi sanadiyyar sace `yan matan Sakandaren Chibok sama da 200,da ke Jihar Barno yau kwanaki 661. Rikicin na `yan Boko Haram, ya dauko asali daga Jihar Barno da ke cikin shiyyar Arewa maso gabas, rikicin da sannu a hankali, ya fadada zuwa kusan dukkan jihohin shiyyar da wasu jihohin kasar nan, kai har ma zuwa wasu kasashen da ke makwabtaka da kasar nan, irin su Jamhuriyar Nijar da ta Benin da Kamaru da Chadi. Har gobe gwamnatin tarayya na begen samun Shugabannin `yan kungiyar ta Boko Haram na hakika, don tattaunawa da su da nufin kawo karshen kashe-kashen rayukar daruruwar  al`umma da wadanda ake jikkatawa da karuwar `yan gudun hijira a ciki da wajen kasar nan.  
Wata afuwar da yanzu ya kamata gwamnatin tarayya ta mayar da hankali a kai ita ce ta barayin shanu da sauran dabbobi da ake fama da ita a wasu sassan jihohin Arewa, irin su Kano da Zamfara da Kaduna da Jigawa da Katsina da Sakkwato da Neja da Kebbi da Barno da Bauchi da sauransu. Sace-sacen da yanzu suka yi sanadin an sace dubun-dubatar dabbobi a irin wadancan jihohi, kuma kusan a kullum sai ka ji an ce an shiga ruga ko gidan gonar wani ko wasu an kore masu bisasansu, a wasu wuraren ma har rayuwa a kan rasa da yi wa matan kauyukan fyade. Alal misali, a wata hira da ya yi da manema labarai a Maiduguri a cikin makon da ya gabata, an ji shugaban gamayyatar wata kungiyar makiyaya kuma shugaban kungiyar Makiyaya ta Al-Hayah, na kasa baki daya Alhaji Ibrahim Mafa, yana fadin cewa tun fara rikicin kungiyar Boko Haram zuwa yanzu an sace masu dabbobi da suka hada da shanu da tumaki da awaki 200773, baya ga membobinsu 1,637, da aka kashe cikin hare-haren satar dabbobinsu a Jihar Borno.
Daga Jihar Zamfara, inda ita ma ta dade tana fama da wannan annoba ta satar dabbobi, inda zuwa yanzu dubban mutanen kauyukan jihar daban-daban suka kaurace wa kauyukansu da dabbobinsu, a zamaan gudun hare-haren masu satar dabbobin da suka mayar da harinsu ba dare ba rana, inda sukan kona kauyukan da yin awon gaba da dabbobin jama`a da yi wa matansu fyade, da inda tsautsayi ya gitta, suke kashe mutanen, an ruwaito Kwamishinan `yan Sandan jihar Mista Femi Ogunbayode, yana tabbatar wa manema labarai cewa, a shekarar da ta gabata ta 2015, kimanin dabbobi da suka hada da shanu da tumaki da awaki har dubu15, suka samu kwatowa, daga barayin dabbobin.
A jihata ta Katsina, inda can ma ake da wancan kwamiitin jami`an tsaro na hadin gwiwa don yaki da masu satar dabbobin, rahotanni sun tabbatar da cewa, zuwa yanzu an kwato dabbobi 11,000, inda aka mayar da dabbobi 9,000 ga masu su.
A Jihar Kano, inda Gwamnan jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci wani biki da aka yi a kauyen Gomo na karamar Hukumar Sumaila, kwanan baya, don yafe wa wasu barayin shanu 39, da suka yi ikirarin sun tuba sun daina satar shanu har abada, bayan sun mika wa jami`an tsaro makamansu, an ji Kwamishinan `yan Sandan jihar Alhaji Muhammadu Musa Katsina, wanda ya  jagoranci Kwamitin hadin gwiwar jami`an tsaro da ke yaki da barayin shanun a jihar, yana fadin cewa, sun kama barayin shanu 253, an kashe 11, an samu kwato shanu 4,000, da awaki da tumaki 1,000, da rakumma 11, da jakuna 19, dabbobin da ya ce tuni aka mayar da fiye da rabinsu ga masu su.
Shi ma Gwamnan jihar Dokta Ganduje, wanda ya yi kakkausan gargadi ga barayin shanun da su tuba kan lallai sun tabbatar da cewa sun daina satar, yana mai kurarin cewa, ‘muddin aka sake kama daya daga cikinsu, to, kuwa zai dandana kudarsa. Gwamnan kuma ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta tallafa wa tubabbun da dukkan abubuwan da suka kamata don su fara sabuwar rayuwa.
Annobar satar shanu, wata mummunar annoba ce da makiyayan kasar nan suka rabu da gani yau kusan shekaru 34, da suka gabata, tunda bayan mummunar cutar shanunnan ta Rinderfest da kasar nan ta yi fama da ita a kusan karshen shekarar 1982, cutar da ta yi sanadiyar mutuwar dubban shanu. Shi kansa wannan yaki da gwamnatocin jihohi suka himmatu akai da har ya kai ana ta hadin gwiwa tsakanin wasu jihohi da suke kan iyaka da juna, Gwamanatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kirkirota, inda ta ba ba da umurni ga jihohin su daura damarar yakin, don haka nike ganin gwamnatin tarayyar ita ta fi cancanta ta bullo da tsarin bayar da afuwa ga barayin shanun da tsarin yadda za ta tallafa musu, musamman kasancewar barayin da suka ce sun tuba a Jihar Kano sun tabbatar da cewa, suna zuwa satar shanu a kusan dukkan sassan jihohin Arewa, sannan kuma sun tabbatar da cewa suna sayar da dabbobin da suka sata a kasuwannanin Arewacin kasar nan da jihohin Kudanci, irin su Legas da Fatakwal da Enugu da sauransu, mai karatu ka ga ke nan barnar ta game kasa da take bukatar daukin gwamnatin tarayya.