Fira Ministan kasar Afhghanistan, Mohammad Hassan Akhund, ya yi kira ga kasashen Musulmi da su aminta da gwamnatin Taliban tare da yin aiki tare da ita a hukumance.
Ya yi kiran ne a ranar Laraba, wata biyar bayan Taliban ta karbe gwamnati a kasar, shekara 20 bayan sojojin kawancen Amurka sun hambarar da gwamnatinta a kasar.
- Yin karin albashin ma’aikata zai haifar da matsala —Gwamnati
- Buhari zai tafi Gambiya bikin sake rantsar da Adama Barrow
“Ina kira ga daukacin kasashen Musulmi su zama a sahun gaba wajen aminta da gwamnatin Taliban a hukumance. Hakan zai taimaka mana wajen samun ci gaba da wuri,” inji shi.
Mohammad Hassan Akhund ya bayyana wa wani taron manema labarai a Kabul babban birnin kasar cewa Afghanistan tana cikin matsananciyar matsalatar koma-bayan tattalin arziki.
A halin yanzu dai babu wata kasa da ta amince da gwamnatin Taliban a hukumance, a yayin da kasashen Yamma ke bibiyar yadda Taliban din za ta gudanar mulkin kasar a wannan karon.
Kasashen Yamma dai na ganin a mulkin Taliban na baya (1996 zuwa 2021) kungiyar ta rika cin zali da cin zarafi sosai gami da tsakura wa mutanen kasar.
A halin yanzu dai kasashen da ke neman kai agaji Afghanistan suna cikin tsaka-ai-wuya, saboda yawancin jami’an gwamantin wucin gadin da Taliban din ta nada suna cikin jerin mutanen da aka sanya wa takunkumi a kasashen duniya.
Amma Akhund ya ce, “Ba ma bukatar taimako daga wani. Ba don jami’an gwamnati muke yi ba, don jama’a muke yi,” yana nufin neman aminta da gwamnatinsu.