An shiga rudani dangane da makomar Mohamed Usman, Jakadan Najeriya a Jamhuriyyar Nijar.
Aminiya ta ruwaito wata sanarwa daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijar tana mai cewa ta dakatar da Jakadan Najeriya tare da wasu jami’an diflomasiyya na ketare.
- Roma na zawarcin dan wasan gaban Chelsea Romelu Lukaku
- Ranar Hausa ta Duniya: Waiwaye kan sunayen Bahaushe da kuma fa’idojinsu
Sanarwar ta ranar Juma’a ta ce an dakatar da Jakadan ne sakamakon kin amsa goron gayyatar wata tattaunawa da Ma’aikatar Harkokin Wajen ta aike masa, lamarin da ya sanya ta ba shi wa’adin sa’o’i 48 ya tattara ina-sa-ina-sa ya koma inda ya fito.
Wannan dai shi ne makamancin dalilin da Ma’aikatar Harkokin Wajen ta bayar cikin wata sanarwa ta daban ta korar Jakadan Jamus a Nijar, Olivier Schnakenberg.
Haka kuma, Gwamnatin Sojin Nijar ta bai wa Jakadan Faransa, Sylvain Itte wa’adin sa’o’i 48 da ya gaggauta barin kasar.
Sai dai kuma a cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijar din ta sake fitarwa, ta yi watsi da sanarwar farko tana mai cewa kanzon kurege ce.
A cewarta, rade-radin da ke yaduwa a dandalin sada zumunta na cewa ta kori Jakadun kasashen Amurka da Jamus da Najeriya ba gaskiya ba ne.
Sai dai ta tabbatar da bai wa Jakadan Jamus wa’adin sa’o’i 48 ya kama gabansa.
Wata majiya a Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Nijar, ta shaida wa Aminiya cewa Gwamnatin Sojin Nijar din ba ta da masaniya game da korar Jakadan na Najeriya.
Majiyar ta ce Gwamnatin Soji wadda ta hambarar da Mohamed Bazoum ta nuna rashin jin dadinta game da lamarin da ta bayyana abin kunya a gare ta.
Wannan dai shi ne dalilin da ma’aikatar ta fitar da wata sanarwar wanda ya nuna akwai alamun rashin hadin kai a tsakanin masu rikr da akalar jagorancin kasar.