✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Sakkwato ta dawo da dalibanta daga Dubai saboda karancin kudi

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta dawo da dalibanta 39 da ke karatu a mayan makaratu daban-daban na kasar Dubai zuwa gida saboda rashin kudin da za…

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta dawo da dalibanta 39 da ke karatu a mayan makaratu daban-daban na kasar Dubai zuwa gida saboda rashin kudin da za ta ci gaba da biya musu kudin karatun.
“Yanayi ya canja, kasa na cikin matsin tattalin arziki, dawo da daliban zai sanya gwamnati ta yi tsimin Naira miliyan 500 da ake kashe musu. Idan kida ya canja dole rawa ya canja. Canji da musayar da muka yi ga daliban ya zama wajibi don tallafa wa sha’anin ilimi a jihar nan. Akwai wurare da dama na bangaren ilimi da ke bukatar daukin gaggawa, kudin za su taimaka ,” inji Gwamnan Jihar, Alhaji Aminu Tambuwal.
Gwamnan ya fadi haka a makon jiya, lokacin da yake karbar rahoton kwamitin da gwamnati ta kafa karkashin Mataimakin Gwamna don duba yadda za a yi canjin har ya samu nasara, ba tare da gurbin kowane yaro ya samu tangarda ba.
“A bara gwamnati ta tura dalibai karatu zuwa Dubai, sai da ta kashe Naira miliyan 400 ga hidimar karatunsu a duk shekara. Tsohuwar gwamnati da ta tura su can da manufa mai kyau ta yi hakan, mu ko a yanzu saboda wannan karaya ta tattalin arziki, ba za mu iya barin su can ba, dole ne mu dawo da su gida.
“‘Mun sanar da iyaye da masu kula da daliban cewa, zuwa yau gwamnati ta kashe fiye da Naira miliyan 500 kan karatun dalibai dubu 17 ’yan salin jiha kan karatunsu a jami’o’i da dama na kasar nan. Akwai nauyi sosai a wannan halin mu iya biyan Naira miliyan 400 ga mutum 39, domin babu kudin. Mun gode wa iyayen yaran da suka fahimce mu kan halin da muke ciki,” inji Gwamnan.