✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fadar Shugaban Kasa ta yi gwanjon jirginta

Gwamnatin Najeriya ta yi gwanjon daya daga cikin jiragen Fadar Shugaban Kasa tana neman mai saye. Tun a Larabar da ta gabata gwamnatin ta sanya…

Gwamnatin Najeriya ta yi gwanjon daya daga cikin jiragen Fadar Shugaban Kasa tana neman mai saye.

Tun a Larabar da ta gabata gwamnatin ta sanya tallan jirgin samfurin Hawker 4000 mai lambar 5N-FGX/:RC 006 a shafukan wasu manyan jaridu na kasar.

Tallan ya ce jirgin, wanda aka fara amfani da shi tun watan Dasumbar 2011, yana da wadata ta daukar fasinjoji tara da ma’aikatan jirgi uku.

An nemi duk masu sha’awar sayen jirgin da su gabatar da bukatarsu a gaban kwamitin sayar da jirgin da ke Ofishin Mai Ba da Shawara kan Harkokin Tsaro na Kasa tare da takardar bankin Dala dubu hamsin.

A shekarar 2016 Gwamnatin Tarayya ta yi gwanjon wasu jiragenta biyu, Falcon 7X da Hawker 4000 domin rage nauyin da ke kanta na kula da su.

Cikin wani rahoto da jaridar The Cable ta wallafa, Gwamnatin Tarayya ta ware kasafin Naira biliyan 73.3 domin kula da jiragen Shugaban Kasa daga shekarar 2011 zuwa 2020.