Gwamnatin Jihar Legas ta bada umarnin rufe makarantar Ojodu Grammar School, wadda wani direban tirela ya kashe wa dalibai sama da 15 a ranar Talata, har zuwa watan Janairun 2022.
Hatsarin dai, wanda ya faru da yammacin ranar Talata, ya jawo asarar rayukan dalibai tare da raunata wasu da dama.
- Rigakafin COVID-19 miliyan 1 ya lalace a Najeriya kafin a yi amfani da shi – Bincike
- COVID-19: An sake samun sabon samfurin Omicron mai wahalar ganewa
Sai dai rundunar ’yan sandan Jihar, ta ce dalibai biyu kacal suka rasa ransu, yayin da kuma dalibai 12 suka ji rauni.
Kakakin ’yan sandan Jihar, Adekunle Ajisebutu ne ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya kara da cewa daliban sun hadu da wasu bata-gari da suka yi kokarin kone ofishin ’yan sanda na yankin Ojodu, sakamakon fusata da suka yi.
Lamarin a ranar Talata ya sanya ’yan kasuwa da ke kasuwanci a yankin rufe shagunansu don gudun tashin-tashina daga bata-gari.