✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Legas ta rufe Kasuwar Alaba

Gwamnatin Legas ta rufe Babbar Kasuwar Alaba, a matsayin wani mataki da take dauka kan kasuwanni masu sakaci da tsaftar muhalli a jihar.

Gwamnatin Legas ta rufe Babbar Kasuwar Alaba, a matsayin wani mataki da take dauka kan kasuwanni masu sakaci da tsaftar muhalli a jihar.

Kwamishinan Muhalli na jihar, Tokunbo Wahab, ya sanar da hakan a safiyar Litinin cewa “An rufe Babbar Kasuwar Alaba da ke yankin Ojo saboda zubar da shara barkata da rashin biyan kudin kwasan shara gami da rashin tsaftar muhalli.”

An rufe kasuwar ta Alaba ce bayan Hukumar Kula da Tsaftar Muhalli ta Jihar Legas (LAWMA) ta rufe wasu kasuwanni kan laifin rashin tsafta.