Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamantinsa za ta kasa sabuwar hukumar da za ta kula da harkar sufuri a Jihar.
Da yake sanar da hakan a yayin kaddamar da taron da Hukumar Sufuri ta Kasa ta gudanar a Kano, Ganduje ya ce sabuwar hukumar za ta game kowane bangare na sufuri tare da magance matsalolin da suka danganci bangaren a jihar.
“Hakan zai taimaka sosai wajen inganta sha’anin sufuri da saukake zirga-zirgar ababen hawa gami da bunkasa harkokin kasuwanci da kuma mayar da birnin Kano daidai da zamani,” inji shi.
Sai dai kuma bai yi bayani ba ko kafa sabuwar hukumar zai kai ga soke Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA).
Ganduje, wanda mataimakinsa, Nasir Yusuf Gawuna ya wakilta, ya ce aiwatar da sabon tsarin sufurin da gwamantin jihar ta bullo da shi zai jawo masu zuba jari tare da inganta zirga-zirgar ababen hawa a jihar.
Da yake nasa jawabin, Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce a yanzu haka wani kwamitin da Gwamnatin Tarayya ta kafa karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, na yin nazari a kan daftarin Tsarin Sufuri na Kasa kafin daga baya a mika shi ga Majalisar Zartarwa ta Tarayya domin amincewa.
Amaechi ya ce Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya ta riga ta kafa kwamitin ministoci da kamfanoni masu zaman kansu domin samar da kyakkyawan jagoranci ta fannin lura da kuma aiwatar da Shirin Inganta Sufuri na Kasa yadda ya kamata.