Hukumar Kula da Wuraren Shakatawa ta Jihar Kano ta bayyana cewa za ta haramta wa masu wuraren shakatawa da Otal-Otal ba wa yara ’yan kasa da shekara 18 dakin kwana.
Shugaban Hukumar Yusuf Ibrahim Lajawa ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a birnin Dabo.
- ’Yan sanda sun kubutar da wanda aka sace a Zamfara
- Bom ya kashe gwamna da sojoji 7 a Afghanistan
- Wata mata ta antaya wa kishiyarta tafasasshen ruwa
Lajawa ya bayyana cewa akwai kudirin dokar a gaban Majalisar Dokokin Jihar Kano wacce da zarar an sanya mata hannu to za ta ba bayar da damar rufe duk wani otal da aka samu da aikata haka ko kuma a daure mai Otel din ko kuma a hada masa duka hukuncin.
Haka kuma ya bayyana cewa duk wanda aka kama da laifin bai wa namiji da mace daki ko hada maza da mata yin wanka a kwamin wanka tare a waje daya shi ma zai iya fuskantar hukuncin dauri.
“Akwai dokoki na Hukumar NDLEA mai hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, to mun yi amfani da su wajen hana sha da tu’ammali da miyagun kwayoyi a wuraren da na ambata,” inji Lajawa.
Ya kara da cewa hukumar tana da ikon kamawa da gurfanar da duk wanda ta samu da yi wa dokokinta karan tsaye.