Kwamitin da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan hana barace-barace a jihar ya ce kwanan nan zai fara jigilar mayar da mabarata zuwa garuruwansu na asali.
Shugaban Hukumar Kula da Barace-Barace ta Jihar, Malam Muhammad Albakari Mika’il ne ya bayyana haka yayin da yake gabatar da wadansu mabarata da kwamitin ya kama a kwanan nan a jihar.
- Kisan Hanifa dabbanci da rashin imani ne —Atiku
- An ceto mutum 2,155 daga hannun ’yan bindigar Zamfara a wata 4
Ya ce sun kama almajirai kimanin 303 a wurare daban-daban a birnin Kano.
Kuma a cewarsa, sun kama mabaratan ne da misalin karfe 12:00 na dare zuwa karfe 4:00 na asubahi duk na rana daya.
Shugaban Hukumar ya ce “Yayin kai wannan samame, mun raba jami’anmu gida biyu.
“Gida na farko ya kai samamen da tsakar dare sai kuma daya gidan ya fita daga tsakar dare zuwa asubahi kamar yadda muka saba yi.
“Mun samu wadansunsu a kan Titin Gidan Gwamna, yayin da wadansunsu kuma muka same su kwance a kan Titin Tarauni.”
Ya ce, “Da muka tambaye su abin da suke yi a wannan waje sai suka gaya mana cewa suna jiran zuwan wani mutum da ba dan kasa ba ne, wanda yake raba Naira bibbiyu.”
Ya kara da cewa sun kama wadansu mabaratan a Unguwar Sabon Gari, inda suka samu yara da dama wadanda yawancinsu suna cikin maye.
“Muna zargin wadanan yara almajirai ne, kasancewar mun samu mafi yawansu tare da kwanukansu,” inji shi.
Ya ce za su mayar da dukkan almajiran da suka kama garuruwansu na asali da kuma wurin malamansu da zarar sun gama tantance su.