Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya ayyana ranar Alhamis, 20 ga watan Agusta, 2020 a matsayin ranar hutu domin murnar zagoyawar sabuwar shekarar Musulunci ta 1441 bayan hijira.
Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar, Muhammad Garba ya fitar ranar Laraba a Kano.
Gwamnan ya yi kira ga al’ummar Musulmin jihar da su yi amfani da lokacin wajen yin addu’o’in neman zaman lafiya da karuwar arziki.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya kawo wa jihar dauki daga annobar COVID-19 da kuma matsin da mutane suke ciki.
Sanarwar ta kuma yi kira ga jama’a da su ji tsoron Allah a cikin dukkannin al’amuransu tare da zama masu yafiya kamar yadda Musulunci ya tanadar.
Ganduje ya kuma ba da tabbacin gwamnatinsa na ci gaba da bunkasa rayuwar al’ummar jihar.
Ana kyautata zaton cewa ranar ta Alhamis ce za ta kasance daya ga watan Al-Muharram, watan farko a shekarar Musulunci ta 1442.
Laraba 19 ga watan Agusta, 2020 ita ce ta zo daidai da 29 ga watan karshe na Zhul Hajji a kalandar Musulunci.