A daidai lokacin da alu’ummar musulmi a duk fadin duniya ke shirye-shiryen bukukuwan karamar Sallah, ma’aikata a jihar Kano sun tsinci kansu a cikin halin rashin tabbas.
Hakan ya faru ne yayin da suka wayi gari an zabtare albashinsu ba tare da cikakken bayani ba.
Binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa ma’aikatan, wadanda suka fara ganin albashin daga ranar Laraba, akasarinsu sun koka cewa an yanke abin da ya kai daga kashi 20 zuwa 30 cikin dari na albashin nasu.
- Mutanen Kano sun yi wasa da annoba ta bi gari —El-Rufa’i
- Ganduje ya yarda a yi sallar Idi da ta Juma’a a Kano
- Gwamnatin tarayya ta tsawaita dokar kulle a Kano
Binciken da aka yi
Hakazalika binciken ya nuna cewa hatta ma’aikatan lafiya da ke sahun gaba wajen yaki da annobar coronavirus a jihar su ma lamarin ya shafe su.
Sun yi korafin cewa idan har gwamnati ba ta basu tallafin rage radadin kullen cutar ba, to kuwa bai kamata ta zabtare albashin nasu a dai-dai wannan lokacin ba.
Yadda ma’aikatan suka nuna rashin amincewa
Ma’aikatan a tattaunawarsu daban-daban sun nuna takaicinsu da wannan batun, su na masu Allah-wadai da lamarin, musamman a lokacin da suke kokarin yin sayayya don bukukuwan Sallah.
Wani ma’aikacin gwamnatin jihar da ya bukaci da mu sakaya sunansa ya ce daukacin ma’akata a jihar sun fada cikin halin rashin tabbas sakamakon wannan ragin ba tare da an sanar da su ba tun da farko.
A cewarsa, ma’aikata a matakin albashi irin nasa an zabtare musu tsakanin Naira 10,300 zuwa 12,00.
Bugu da kari, wani ma’aikacin a ma’aikatar kananan hukumomi, ya ce an yanke masa Naira 7,600 daga nasa albashin.
Daga bangaren kungiyar ‘yan kwadago
To sai dai a yayin tattaunawarsa da Aminiya ta wayar salula, shugaban kungiyar ‘yan kwadago ta jihar Kano, Kwamared Kabiru Ado Minjibir ya ce kungiyarsu ba ta da masaniya a kan wannan labarin.
Ya ce “Gwamnati ba ta sanar da mu ba, saboda haka za mu bincika mu gano gaskiyar wannan lamarin.
“Tuni muka umurci kungiyoyin mu na NLC, TUC da NJC da su bincika lamarin, idan muka gama za mu kira taron gaggawa don tattauna batun”, in ji Minjibir.
A kan ko kungiyar ta su za ta dauki wani mataki a kan lamarin, shugaban ‘yan kwadagon ya ce tattaunawar da za su yi ce kadai za ta tabbatar da hakan.
To sai dai duk kokarin da Aminiya ta yi na ji daga bakin gwamnatin jihar Kano ya ci tura sakamakon Shugabar Ma’aikatan jihar Kano, Hajiya Binta Lawan Ahmed bata amsa wayar da mu ka kira ba kuma ba ta amsa rubutaccen sakon da muka tura mata ba har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Idan dai za’a iya tunawa a makon da ya gabata ne gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da rage albashin dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin dari.
An rage sakamakon matsin tattalin arzikin da annobar ta jefa jihar, musamman ta bangaren samun kudaden shiga.