✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta yi watsi da dokokin haraji

Mataimakin Gwamnan, ya ce Jihar Kano ba za ta aminta da duk wata doka da za ta cutar da al'ummarta ba.

Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana matsayarta kan sabbin dokokin haraji da ake tattaunawa a Majalisar Dokokin Najeriya.

Mataimakin Gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya bayyana wannan matsayi a lokacin bikin sabuwar shekara ta 2025 da aka gudanar a Filin Mahaha da ke Ƙofar Naisa.

Wannan bayani ya fito ne ta hannun kakakin yaɗa Labaran Gwamnan, Ibrahim Garba Shu’aibu.

Gwarzo, ya ce: “Waɗannan dokokin haraji ba su ne mafita ga matsalolin tattalin arziƙinmu ba.

“Jihar Kano ba ta yarda da kowace doka da za ta cutar da walwalar al’ummarmu.”

Ya yaba wa jajircewar al’ummar Kano wajen fuskantar ƙalubalen tattalin arziƙi, inda ya ce sam harajin bai dace ba.

Ya ƙara da cewa kamata ya yi gwamnati ta fi mayar da hankali kan yaƙi da talauci da yunwa, musamman a yankin Arewa, wanda ke fama da tsadar rayuwa da rashin tsaro.

Mataimakin Gwamnan, ya kuma jaddada nasarorin gwamnatin Kano a ɓangarorin lafiya, ilimi, samar da hanyoyi, da tallafin karatu zuwa ƙasashen waje.

Ya tunatar da al’umma hukuncin Kotun Ƙoli a watan Janairu 2024 wanda ya tabbatar da Gwamna Abba a matsayin halastaccen gwamnan Jihar Kano.

Hakazalika, Gwarzo ya yi bikin dawowar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, a shekarar 2024, inda ya ayyana hakan a matsayin muradin jama’a.

Ya jaddada cewa ikon naɗa sarki ya rataya ne a wuyan gwamnan Jihar Kano kaɗai, sannan ya buƙaci masu shiga harkokin masarautar Kano su mutunta doka da kuma tabbatar da zaman lafiya.

Har ila yau, ya yi kira ga Kanawa da su kasance masu haɗin kai da fatan alheri ga juna.

“Muna fatan 2025 ta zamo shekarar ci gaba da wadata ga kowa. Tare, za mu gina Kano mai inganci.”